Kano: Za a Fara biyan malamai firamare a jihar Kano

Kano: Za a Fara biyan malamai firamare a jihar Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta ce zata fara biyan malamai makarantar firamare waɗanda aka kara wa girma a shekara 2014, 2015, 2016 da kuma 2017 a jihar

- Malamai 44, 654 da kuma sauran ma’aikata wadanda ba koyarwa suke ba za a fara biya a watan nan

- Majalisar zartarwar jihar ta umarci ma'aikatar kudi da ofishin Akanta Janar da su tabbatar da cewa an aiwatar da biyan karin albashin malaman daga watan Yuni, 2017

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta amince da kudi naira miliyan 578 domin biyan malamai makarantar firamare 44, 654 da kuma sauran ma’aikata wadanda ba koyarwa suke ba a karkashin “State’s Universal Basic Education Board”.

Kwamishinan labarai, Malam Muhammad Garba, ya bayyana haka a ranar Talata, 20 ga watan Yuni a cikin wata sanarwar sakataren labarai ga gwamnan jihar, Malam Ameen Yassar.

Ya ce adadin kudin zai biya waɗanda aka kara wa girma a 2014, 2015, 2016 da kuma 2017.

Kano: Za a Fara biyan malamai firamare a jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano, Dakta Umaru Abdullahi Ganduje

Ya bayyana cewa, majalisar zartarwar jihar, a karkashin shugabancin mataimakin gwamnan, Farfesa Hafiz Abubakar, ta amince da biyan, wanda za a fara daga watan Yuni 2017, bayan tattaunawa tare da wakilan kungiyar ma’aikata wato Nigerian Labor Congress (NLC) da kuma kungiyar malamai na kasa wato Nigerian Union of Teachers (NUT).

KU KARANTA: Sanata Musiliu Obanikoro ya canza shake zuwa APC

NAIJ.com ta ruwaito cewa bayan jerin tattaunawa tsakanin gwamnatin jihar da kuma kungiyoyin kwadago, musamman a kan biyan kudaden ma’aikatan, a halin da ake ciki yanzu an yi yarjejeniyar cewa malamai zasu yafe kudin alawus-alawua nasu.

Kwamishinan ya ce: " A watan Mayu 2017, gwamnatin jihar na biya malamai firamare biliyan 2. 33, amma a halin yanzu bayan ci gaba da aka samu, albashinsu ta tashi zuwa biliyan 2. 91.”

A cewar kwamitin, majalisar zartarwar jihar ya umarci ma'aikatar kudi da ofishin Akanta Janar da su tabbatar da cewa an aiwatar da biyan karin albashin malamai daga wannan watan Yuni, 2017 nan da nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zanga-zangar bikin tunawa da ranar mata a Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad
NAIJ.com
Mailfire view pixel