Sanata Musiliu Obanikoro ya canza shake zuwa APC

Sanata Musiliu Obanikoro ya canza shake zuwa APC

Tsohon karamin ministan tsaro, Musiliu Obanikoro ya canza sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

Obanikoro ya alanta wannan abu ne a wata hira da manema labarai yau Talata a jihar Legas.

Zaku tuna cewa a ranan 7 ga watan Mayu Obanikoro wanda yayi takaran gwamna a jihar Legas yace ba da dadewa ba zai koma jam’iyyar APC.

Majiya sunce ya kasance yana ganawa da shugabannin jam’iyyar APC domin yunkurin komawa jam’iyyar.

YANZU-YANZU: Sanata Musiliu Obanikoro ya canza shake zuwa APC

YANZU-YANZU: Sanata Musiliu Obanikoro ya canza shake zuwa APC

A bangaren jam’iyyar APC kuma, sun tarbe shi da hannu biyu saboda goyon bayan da babban jigon APC, Ahmed Tinubu, ya bayar.

KU KARANTA: Wani azzalumi ya bugawa yaro kusa a kai

Amma an tattaro cewa da farko, Tinubu ya nuna rashin amincewa da dawowan Obanikoro APC bayan sunyi baran-baran kimanin shekaru 10 da suka gabata ya koma PDP. Amma Tinubu ya karbi sulhu ne bisa ga manyan da sukayi masa Magana wanda ya kunshi sarkin Legas.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel