Dan ƙasa na gari abin koyi: Idan ka ji abinda Dangote yayi, zai burge ka

Dan ƙasa na gari abin koyi: Idan ka ji abinda Dangote yayi, zai burge ka

- Kamfanin Dangote ta mika wani tsohon direbanta hannun hukumar kwastam

- Direban ya kwashi kayayyakin fasa kauri

Kamfanin siminti na Dangote dake garin Ibese, na jihar Ogun yace sun kama wata motarsu a garin Ibadan dauke da kayayyakin fasa kauri, kuma suka ta mika shi ga jami’an hukumar hana fasa kauri ta kasa, inji jaridar Daily Trust.

Yayin da ake mika direban da yaron motar ga hannun jami’an kwastam din, mataimakin shugaban tsaro na kamfanin, Ali Garba yace sun kama tsohon direban kamfanin Ismaila Abubakar yana tuka motarsu dauke da kaji yankakku, ya nufi jihar Edo.

KU KARANTA: Gagararran mai garkuwa da mutane, ‘Evans’ ya kai 'yan sanda maɓuwayrsa (HOTUNA)

Ali Garba yace direban motar na hakika, Nasiru H Ahmed yayi lodin buhunan 900 ne na siminti a ranar 2 ga watan Yuni 2017. Amma sai a garejin Kara, Nasiru ya sauka ya wuce birnin gwari, inda ya bar motar a hannun yaran motarsa Bilyaminu Abdullahi da Bashiru, tare da tsohon direban da kamfanin ta sallam Isma’ila Abubakar.

Dan ƙasa na gari abin koyi: Idan ka ji abinda Dangote yayi, zai burge ka

Motar Dangote

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito daga bisani ne Isma’ilan ya tuka motar zuwa garin Bini don sauke simintin bayan ya cire na’urar bin diddigin motocin kamfanin, daga nan kuma sai yayi Iyana Isolo a garin Legas inda ya kwashi kaji da nufin zia kais u jihar Edo akan kudi N350,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yansanda sun je mabuwayar mai satar mutane:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel