Yadda aka kai ma Musulmai masallata hari a birnin Landan (Bidiyo)

Yadda aka kai ma Musulmai masallata hari a birnin Landan (Bidiyo)

- An saki bidiyon yadda aka kai ma musulmai hari a Landan

- An bayyana sunan dan ta'addan daya kai harin

Wani harin ta’addanci da aka kai ma Musulmai masallata a kasar Ingila, birnin Landan yayi sanadiyyar mutuwar mutum daya, tare da jikkata wasu da dama yayin da maharin ya afka musu a mota jim kadan bayan fitowarsu daga sallar Isha.

Sai dai, yansanda sun samu nasarar kama wanda ake zargi da kai harin mai suna Darren Osborne mai shekaru 47 dan asalin kasar Birtaniya, bayan da jama’a suka yi ram da shi, kuma yanzu haka yansanda na tuhumarsa da aikata laifin ta’addanci.

KU KARANTA: Fasto yayi hasashen mutuwar Fani Kayode, kamar yadda shima yayi hasashen mutuwar Buhari

Dayake yaci duka a hannun jama’a, a yanzu haka yana asibiti yana samun kulawa, amma da zarar an sallame shi za’a gurfanar da shi gaban kotu, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Yadda aka kai ma Musulmai masallata hari a birnin Landan (Bidiyo)

Musulmai masallata hari a birnin Landan

A wani hannu kuma, Firaiministan Birtaniya Theresa May tayi Allah-wadai da harin ta’addancin, inda ta bayyana shi da ‘Abin takaici’, sa’annan tace “Mun dade muna kawar da idanunmu daga masu tsatstsauran ra’ayi.”

Ga bidiyon harin nan, kamar yadda BBC Hausa ta daura shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda wani mutumi ya muslunta:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel