Kwakƙwaran naushi ya aika da shahararren ɗan dambe Lahira (Hoto)

Kwakƙwaran naushi ya aika da shahararren ɗan dambe Lahira (Hoto)

- Wani sdan dambe mai suna Tim Hague ya riga mu gidan gaskiya

- Tim Hague ya mutu ne sakamakon dukan kawo wuka daya sha

Wani shahararren dan dambe mai suna Tim Hague, wanda a baya yana damben hannu da kafa ne ya riga mu gidan gaskiya bayan daya ci duka a hannun abokin karawansa a ranar Juma’a 16 ga watan Yuni.

Shi dai Tim Hague wanda bai dade da shiga harkar damben hannu kadai ba yayi fadansa na farko ne da Pat Barry inda ya samu nasara akansa, amma tun daga nan bai sake samun nasara a sauran fada guda uku da yayi a bayan nan.

KU KARANTA: Hotunan taron dandazon ýan PDP da suka sauya sheka zuwa APC a Fatakwal

Kafin mutuwarsa, Tim Hague ya fafata ne da Mladen Miljas da Adam Braidwood, inda bayan fadan sa na karshe ne ya fita da kafarsa daga filin, amma koda yaje gida, sai hali ya gagara, aka garzaya da shi asibiti.

Kwakƙwaran naushi ya aika da shahararren ɗan dambe Lahira (Hoto)

Tim Hague

A asibitin ne fa ya shiga halin kakanikayi, daga nan sai yace ga garin kun an, inda a ranar Lahadin data gabata aka sanar da mutuwarsa ta hannun iyalansa, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mabuyar dan fashin nan mai satar mutane:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel