Karyewar gadar Mokwa zuwa Jebba: Za’a share makonni 2 ana gyara

Karyewar gadar Mokwa zuwa Jebba: Za’a share makonni 2 ana gyara

- Hukumar sufurin jiragen kasa na Najeriya (NRC) ta ce za a dauki tsawon sati biyu a gyaran babbar gadar da ta hade garin Mokwa da Jebba

- Ruwan sama mai karfi da aka yi ya karya gadar titin jirgin kasa da hanyar mota tsakanin Mokwa zuwa Jebba kuma karyewar gadar ya haifar da kalubale wajen sufurin jiragen kasa

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar sufurin jiragen kasa na Najeriya (NRC) ta ce za a dauki tsawon sati biyu a gyaran babbar gadar da ta hade garin Mokwa da Jebba sakamakon ruwan sama da ya lalata gadar jirgin kasan da ta mota a babbar hanyar da ta hada yankin arewacin Najeriya da kudanci a jihar Niger.

Yakubu Mahmud, wanda shine jami’in hulda da jama’a na hukumar ya bayyana cewa ruwan sama mai karfi da aka yi ya karya gadar titin jirgin kasa da hanyar mota tsakanin Mokwa zuwa Jebba kuma karyewar gadar ya haifar da kalubale wajen sufurin jiragen kasa daga Lagas zuwa Kano da kuma motocin da ke jigila daga kudu zuwa arewacin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Abin al’ajabi: Wani masallaci da mata da maza ke ibada a tare

Karyewar gadar Mokwa zuwa Jebba: Za’a share makonni 2 ana gyara

Gadar da ta rufta

Motocin da suka fito daga Lagas a yanzu haka dai ba su iya wuce garin Jebba cikin jihar Kwara, yayin da wadanda suka fito daga yankin arewaci ba su iya wuce garin Mokwa a jihar Niger.

Karyewar gadar nan na zuwa ne a yayin da ake dab da gudanar da bikin Sallah kuma aikin gyaran gadar zai dauki tsawon mako biyu domin injiniyoyi suna can suna aiki dare da rana.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel