Osinbajo ya yanke shawarar dage zamansa da sarakunan Arewa

Osinbajo ya yanke shawarar dage zamansa da sarakunan Arewa

- An dage zaman shugaba Osinbajo da Sarakunan gargajiya na arewa

- Ana ta cece-kuce tsakanin kudu da arewa

- Ana zargin shugaba Osinbajo da bagaranci

A ci gaba da tattaunawar zaman lafiyar kasa tsakanin kabilun kudu da arewa, bayan ganawa da yayi da sarakunan kudancin kasa, shugaba Osinbajo ya dage ganawarsa da sarakunan arewa, saboda suna bukatar hutawa bayan shan ruwa da suka yi tare da shi a jiya.

Zaman na jiya dai da suka yi na shan shayi ne, kuma bayan ansha ruwa, sai aka bukaci a huta domin su sarakunan su samu suje neman daren lailatil kadari, da niyyar yau da hantsi za'a ci gaba da zaman.

KU KARANTA KUMA: 'Arewa ce ke juya mukaddashin Buhari Osinbajo' inji wani jigon APGA

Osinbajo ya yanke shawarar dage zamansa da sarakunan Arewa

Osinbajo ya yanke shawarar dage zamansa da sarakunan Arewa

Sai dai har yanzu ba'a iya kama masu rura wutar bangarancin ba, daga kudu ko arewa, hasali ma, masu irin wannan taga-taga ba lallai suna sauraro ko girmana shuwagabannin nasu ba, in dai da gaske sun shirya tafka wata aika-aika a wa'adin da suka debawa juna.

A yau dai ana sa rai sarakunan zasu sake zama tare da shugaba Osinbajo don shawo kan matsalar bangarancin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel