'Arewa ce ke juya mukaddashin Buhari Osinbajo' inji wani jigon APGA

'Arewa ce ke juya mukaddashin Buhari Osinbajo' inji wani jigon APGA

- Ana cece-kuce tsakanin kabilun kasar nan

- Arewa ta rabu kan batun kabilar Ibo

- 'Mukaddashin shugaban kasa na bangaranci'

A kokarinsu na tada kurar siyasa, manyan kasa da manyan siyasa, na kara yamadidi da zance wai lallai akwai bangaranci a tattare da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wasu daga arewa na cewa ya karkata yana nada mutan kudu, na kudun kuma na cewa ya fi kyautata wa arewa.

Hakan ta sake fitowa daga wani jogo a jam'iyyar APGA, reshen jihar Anambara, wadda ita ce jam'iyya da kabilar Ibo suka fi runguma, Ekene Enefe, wanda yayi tsokaci kan batun barazanar korar kabilar Ibo da wasu suka yi, inda yace rashin kame samarin arewar lalle bangaranci ne daga hannun shugaban.

'Arewa ce ke juya mukaddashin Buhari Osinbajo' inji wani jigon APGA

'Arewa ce ke juya mukaddashin Buhari Osinbajo' inji wani jigon APGA

Enefe dai ya yi kashedin da kada gwamnati tayi sakaci da batun, tunda har yanzu samarin basu shiga hannu ba, kuma basu fasa batun korar kabilun kudun ba. A cewar sa, wasikar baya-bayan nan da samarin suka rubuta ga shi Osinbajo fa tana da hadari, inda suka ce lallai Osinbajo ya gaggauta barin kabilar ibo kafa kasarsu ta Bayafara a kudu.

"Babban abin takaici ne ace wai har yau an kasa kama samarin, kuma suna ta nanata kiran nasu na koras kabilu daga arewa, kuma gwamatin tarayya ta kasa cewa komai ko kame su da kaisu jarun, wannan ya nuna arewa ce ke da iko da Farfesa Yemi Osinbajo."

Ya kara da cewa, "wannan ba shine karon farko da aka saba yi wa kabilar Ibo wannan barazana ba, kuma take zamowa bala'i. Dole gwamnati tayi maza-maza ta kame su samarin ta garkame, wannan ne kawai zai hana irin hakan sake faruwa, in kuwa ba haka ba, lallai arewa ke jujjuya Osinbajo."

Ana dai fatan hana wutar rikicin kabilanci ruruwa tsakanin al'umma, ta hanyoyi daban daban, daga kabilun hausawan har ma na kudu, masu son zaman lafiya, harma da manyan yan siyasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel