Gwamnatin tarayya ta saki biliyoyin kudi daga kasafin kudin bana don manyan ayyuka

Gwamnatin tarayya ta saki biliyoyin kudi daga kasafin kudin bana don manyan ayyuka

- An sako Naira Biliyan dari kusan hudu don manyan ayyuka

- Kasafin kudin bana don habaka tattalin arziki aka yi shi

- Manyan ayyuka ne zasu lakume kasafin kudin bana

An saki biliyoyin kudi daga cikin kasafin kudin bana da shugaban kasa Osinbajo ya rattabawa hannu, a cewar Ministar kudi Kemi Adeosun. Kudaden da yawansu ya kai biliyan dari ukku da saba'in, zasu je su biya 'yan kwangila, kudaden manyan ayyuka.

Ministar ta ce kudaden zasu je ma'aikatun gwamnati su biya ayyukan da ke cikin bajat, ta kuma yi kashedin kada wata ma'aikata ta je ta biya wasu kudade ko ta shiga kwangila da dalar kasar Amurka, domin kudin zai surare a banza, kuma tsadar kwangilar zai karu.

KU KARANTA KUMA: Abin al’ajabi: Wani masallaci da mata da maza ke ibada a tare

Gwamnatin tarayya ta saki biliyoyin kudi daga kasafin kudin bana don manyan ayyuka

Gwamnatin tarayya ta saki biliyoyin kudi daga kasafin kudin bana don manyan ayyuka

Ta kuma kara da cewa, "mun gaji ayyuka da dama daga tsoffin gwamnatoci kuma muna so mu karasa su, domin barinsu bashi da wata fa'ida sai asarar kudin jama'a."

Ta ce kuma a bayar da kwangiloli ga wadanda suka cancanta, wadanda ke da takardun cika ka'idojin aiki da biyan haraji.

Ana dai cikin shekara ta ukku a mulkin jam'iyyar APC, kuma ma'aikatan gwamnati na kokarin ganin sun yi wani katabus ga talakka saboda lokacin zabe na kara karatowa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel