Ja'iri Evans na so a yafe masa garkuwa da mutane da yayi

Ja'iri Evans na so a yafe masa garkuwa da mutane da yayi

- Ni fa ina tsoron Allah kuma ina so ya yafe mun, shi yasa nake karanta Baibul kullum

- In an yafe min zan koma kama masu sace mutane

- Na gaya wa mata ta muggan kwayoyi nake sayarwa

A yayin da aka kaishi gidan da yake ajje mutane don neman kudin fansa, a jihar Lagos, gidan da ya kama yake biyan haya tun 2010, Evans yace a yanzu yayi nadama kuma ma zai dinga taya 'yansanda aikin kamo masu garkuwa da mutane.

A cewar sa, shi ustazu ne mai karanta Bible a kullum, kuma yana zuwa coci, sannan yakan saka matarsa ta biya wa yara Ikiliyarsa ta Baibul, domin Allah ya yafe masa laifukansa.

Evan, ya kuma ce lallai ya taba gaya wa matarsa cewa shi fa mai saida muggan kwayoyi ne, inda tace ya daina domin hakan babu kyau.

Ja'iri Evans na so a yafe masa garkuwa da mutane da yayi

Ja'iri Evans na so a yafe masa garkuwa da mutane da yayi

Ya kuma ce sau da dama yakan azabtar harma da harbin mutane don su fito masa da kudin fansa. A inda ya ce ya tara makudan kudade daga wannan harkar.

A cewarsa dai, ko yanzu ya mutu yasan zalamar son kudinsa ce ta jawo masa, yace ba tsafi yake ba, kawai waya ake a kawo masa kudin fansa.

Ja'iru dai ya laka wa mahaifinsa laifi da cewa shi ya cuce shi ya hana shi ilimi sa'ilin da yana karami, ya kuma watsar dashi, domin haka sai dai a taimaka ayi masa afuwa. ya kuma kara da cewa wai ya baiwa mahaifin jari da kudin sata don ya yi gonar aladu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel