Samarin arewa sun fitar da yan takarar shugaban kasa

Samarin arewa sun fitar da yan takarar shugaban kasa

- Wasu samarin arewa sun ce lallai sai an tsayar da dan arewa takara a 2019

- Sun yi kashedi ga jam'iyyu kan lallai sai an tsayar da dan arewa daga kowacce jam'iyya

- Sun bada sunayen mutum 11 sunce a zabo biyu daga ciki

Gamayyar wasu kunyoyi na samarin arewa sun sake barota, inda suka yi kashedin lalle sai dai a sake tsayar da dan arewa takara ya karasa mulkin da ake sawa rai shugaba Buhari zayyi na shekaru takwas muddin kuwa ba haka ba, sunje jam'iyyu zasu yi asarar kuri'un arewa.

Sun bada sunayen gagga-gaggan yan siyasa na arewa da suka ce lalle sai a cikinsu ne za'a zabo yan takarar shugaban kasa, mutum goma sha day da suka hada da Alh. Atiku Abubakar, Alh. Sule Lamido, Alh. Nasiru El-Rufai, Alh. Rabiu Kwankwaso, da dai sauransu. Wannan sanarwa ta fito ne daga hannun sakataren kungiyar Mr. Elliyot Afiyo.

KU KARANTA KUMA: Mafi yawan dabinon da aka karkatar yana jihar Zamfara

Samarin arewa sun fitar da yan takarar shugaban kasa

Samarin arewa sun fitar da yan takarar shugaban kasa

Wata Kungiyar mai suna Northern Youth leaders forum (NYLF) wato Kungiyar shugabanin samarin arewa ta fitar da sunayen mutanen goma sha daya wanda Kungiyan zata mara ma baya domin 'dare wa kujerar shugabancin Najeriya a shekarar 2019.

NAIJ.com ta tattaro cewa shugaban kungiyar mai suna Elliot Afiyo ya bada sunayen mutanen kamar haka;

1. Alhaji Atiku Abubakar (tsohon mataimakin shugaban kasa)

2. Gwamna Ibrahim Hassan Dankumbo na Jihar Gombe

3. Gwamna Aminu Tambuwal (Sokoto)

4. Dr. Bukola Saraki (shugaban majlisan dattijai na kasa)

5. Alhaji Sule Lamido (tsohon gwanman Jigawa)

6. Mal. Nasir El-Rufai

7. Senata Rabiu Musa Kwankwaso

8. Senata Ali Modu Shariff

9. Gwanma Ibrahim Shettima

10. Gwamna Abdulaziz Yari

11. Alhaji Tanimu Turaki da kuma Senata Bala Muhammad

Shugaban ya cigaba da cewa sun zabi wannan mutanen domin jajircewarsu da aiki da gaskiya.

"Muna so mu kara jadada ma jama'a cewa baza mu yarda mulki ya koma kudu ba" inji dan kungiyar.

Kungiyar tayi kira ga samari da 'yan siyasan arewa da mara wa 'yan arewa baya idan zaben 2019 ya zo.

"Mun mika sunayen mutanen da muka tatantance zuwa ga iyayen kungiyar tamu domin su sake tankade da rairaya su fitar mana da mutane biyu wanda zamu sanar da jama'a a taron kungiyar na kasa ta za'ayi a watan satumba na wannan shekaran" inji Comrade Afiyo.

Kungiyan har illa yau tayi kira ga samarin arewa da su guji tada fitina. Akan batun koran kabilar ibo daga arewa kungiyar tace bata goyon bayan hakan amma tace samarin ibo ne suka fara wa mutanen arewa gori har ma da kiran su cima zaune duk da kowa ya san cewa babu al'ummar da zata iya rayuwa ba tare da hulda da wata kabilar ba.

Daga karshe kungiyar tayi kira ga Shugaban kasa mai rikon kwarya Osinbanjo da ya binciko shawarwarin da mutanen kasa suka bada a taron kasa da akayi a mulkin baya don samun mafita.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel