Mafi yawan dabinon da aka karkatar yana jihar Zamfara

Mafi yawan dabinon da aka karkatar yana jihar Zamfara

- Rahotanni sun kawo cewa shugabar hukumar kula da 'Yan gudun Hijira ta kasa, Sadiya Umar Farouq tana bayan abin kunyar da aka tafka na sace dabinon da Saudiyya ta ba Najeriya a matsayin kyauta

- Bincike ya nuna cewa an tura mafi yawan kaso na dabinon zuwa jihar Zamfara

- Majiya mai inganci tace Sarkin Gusau da Sarkin Zurmi da Sarkin Birnin Magaji dana Kaura sun karbi kaso mafi yawa daga dabinon

Binciken da Jaridar Daily Nigerian ta gudanar ya nuna cewa shugabar hukumar kula da 'Yan gudun Hijira ta kasa, Sadiya Umar Farouq tana bayan abin kunyar da aka tafka na sace dabinon da Saudiyya ta ba Najeriya a matsayin kyautar azumin Ramadan.

Sadiya wacce jigo ce a jam’iyya mai mulki ta APC,kuma wakiliya a kwamitin kamfen Shugaban Kasa ta fito daga jihar Zamfara.

Bincike ya nuna cewa an tura mafi yawan kaso na dabinon zuwa jihar Zamfara inda aka ajiye shi a dakunan ajiye kayayyaki yayin da aka rarraba saura ga Sarakunan gargajiya.

KU KARANTA KUMA: Siyasa: Duba Samari 11 da suka zama sanatoci

Mafi yawan dabinon da aka karkatar yana jihar Zamfara

Mafi yawan dabinon da aka karkatar yana jihar Zamfara

Majiya mai inganci tace Sarkin Gusau da Sarkin Zurmi da Sarkin Birnin Magaji dana Kaura sun karbi kaso mafi yawa daga dabinon.

"Yanzu da muke magana, akwai dakin ajiye kaya (Sito) a Gusau inda shugabar ta ajiye kayan agaji tare da Dabinon" a cewar wata majiya da ya nemi a sakaya sunansa.

Karin matsala shine, daraktan mulki da kudi na hukumar Bashir Ahmad dan Zamfara ne, duk kulle-kullen da ake yi a hukumar sune keyi.

Ya kamata su yi cikakken bayani kan lamarin.

Da jaridar Daily Nigerian ta nemi jin ta bakin Mai magana da yawun hukumar, Halima Musa, ta karyata hada baki da Shugabar hukumar wajen sayar da Dabinon.

Halima tace koda aka raba dabinon Shugabar hukumar na Saudiyya, mun rarraba shi ga 'Yan gudun hijira ne kawai.

A karshe mu a wurin mu, babu ko da kwaya da aka sayar a kasuwa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel