Za a fatattako Dino Melaye daga Majalisar Dattawa

Za a fatattako Dino Melaye daga Majalisar Dattawa

– Ana nema a maido Sanata Dino Melaye gida

– Za a iya yi wa Sanata Melaye kiranye daga Majalisa

– Mutane sama da 180,000 su ka nemi hakan

Sanata Dino Melaye na kara shiga cikin matsala a halin yanzu. Kun dai ji mutane sama da 180,000 su na nema su yi masa kiranye. Yanzu ya rage Hukumar zabe ta san wannan halin da ake ciki.

Za a fatattako Dino Melaye daga Majalisar Dattawa

Sanata Dino Melaye a wani zaman da Shugabannin Majalisa

Wani Jami’in Hukumar zabe na INEC ya bayyana cewa mutane 188,588 su ka sa hannu inda su ka nemi a maido Sanata Dino Melaye gida daga Majalisar Dattawa inda yake wakiltar mazabar sa ta Yammacin Kogi.

KU KARANTA: Osinbajo yayi sabon nadi; karanta ka sha labari

Za a fatattako Dino Melaye daga Majalisar Dattawa

Abubuwa na cigaba da cabewa Dino Melaye

Yanzu dai ya rage a sanar da Hukumar zabe na kasa watau INEC domin a dauki mataki na gaba. A dokar tsarin mulkin kasa dai ya halatta Jama’ar da ke mazaba su kira duk ‘Dan Majalisar da ba su amince da shi ba.

Kwanaki kun ji cewa Sanata Dino Melaya ya ga uwar bari yayin da wasu su ka kai masa hari yayin da yake wani taro a wata makaranta da ke Garin Lokojo. Jama’a ne dai su kai hari da bindiga da wasu makamai a wurin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Batun rattaba hannu kan kasafin kudin bana

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel