An kama lodi-lodi na shinkafar fasa-kauri

An kama lodi-lodi na shinkafar fasa-kauri

- Hukumar kwastam sun sake sabon kamu!

- An kama buhunhunan shinkafa yar gwamnati guda dari biyu da ashirin

- Masu fasa-kauri sun boye shinkafa cikin zannuwan gada da sauran kayan gida.

Harkar fasa-kauri dai abu ne wanda ya mamaye duniya amma duk da haka jami'an tsaro na kwastam basu kasa a gwiwa domin kokarin yaqi da wannan kazamiyar sana'a. A yunkurin hakan ne hukumar kwastam na Najeriya reshen Lagas tayi wani kamu.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar Kwastam dake birnin Ikeja, zone A Jihar Legas mai suna Jerry Attah ya bada sanarwa nasarar cafke motar DAF lamba XT- 223 EKY a babban hanyan Legas zuwa Ibadan mai dauke buhunhunnan shinkafa wanda yawan su ya kai dari biyu da ashirin.

An kama lodi-lodi na shinkafar fasa-kauri

An kama lodi-lodi na shinkafar fasa-kauri

Masu fasa-kaurin dai sun lullube shinkafar da zannuwan gado, resho, da kuma wasu kayan masarufi. Toh, amma daya ke dubun su ta cika, jami'an kwastam a karkashin jagorancin AC Adahunse R.A sun bincika motar inda suka gano shinkafar.

An kama lodi-lodi na shinkafar fasa-kauri

An kama lodi-lodi na shinkafar fasa-kauri

Ita dai shinkafar da aka kwace darajar kudin harajin ta ya N2,713,491.

Daga bisani jami'in ya hori jama'a da su guji irin wannan aika-aikan domin tana da hadari ga mutane kuma tana dakile tatalin arzikin kasa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel