Malam Nasir El-Rufai yace 'dole a koma gida'

Malam Nasir El-Rufai yace 'dole a koma gida'

- An yi kira ga gwamnatoci da su dena sayo kayan daga waje

- Malam Nasir El-Rufai ya ce dole a koma gida

- Malam El-Rufai ya yaba da kimiyyar daliban Takanikal

A shafinsa na sadarwar zamani, wato fesbuk, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya saki wasu hotuna da ke nuna shi a kan wasu kujeru da daliban makarantar Takanikal, ta Kaduna, suka kera inda yace ya kai ziyara ne makarantar.

KU KARANTA KUMA: Abin al’ajabi: Wani masallaci da mata da maza ke ibada a tare

Malam Nasir El-Rufai yace 'dole a koma gida'

Malam Nasir El-Rufai yace 'dole a koma gida'

A cewar gwamnan, gwamnatinsa zata tallafawa makarantun na kere-kere, kuma ma kudin da jiha ke kashewa domin sayo kujeru da tebura na daga 'yan kwangila ya ninninka kudaden da ake samun kujerun masu kwari a hannun su wadannan dalibai.

Malam Nasir El-Rufai yace 'dole a koma gida'

Kujerun da daliban suka kera

"Dole a koma gida, muna samun araha sosai wajen sayan kayan kere-kere daga wadannan makarantu, kuma munyi alkawarin zamu tallafa musu.' Ya wallafa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel