‘Yar sarkin Kano Gimbiya Siddika na shirin haihuwa

‘Yar sarkin Kano Gimbiya Siddika na shirin haihuwa

- Yar sarkin Kano na shirin haihuwar dan ta na fari tare da mijinta

- Ma’auratan sunyi kasaitaccen aure a shekarar 2016

- Sun buga kyawawan hotuna yayinda suke bikin murnar zagayowar ranar haihuwa a lokacin bude baki

Gimbiya Fulani Hafsat Siddika da mijinta Abubakar Kurfi na shirin tarban dansu na fari tare a matsayin ma’aurata. Ma’auratan sun shiga dakin aure a watan Disamba na shekarar 2016 sannan kuma alamu sun nuna tana dauke da juna biyu yayinda suka halarcin bikin zagayowar ranar haihuwa na wasu abokai bayan shan ruwa.

An buga kyakkyawan hoton ne a shafin zumunta sannan kuma an nuno aminnan guda biyu, Siddika wacce ta kasance ‘yar sarkin Kano da kawarta na dauke da juna biyu.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda wani malamin musulunci ya daure dalibinsa da mari (HOTUNA)

‘Yar sarkin Kano Gimbiya Siddika na shirin haihuwa

‘Yar sarkin Kano Gimbiya Siddika na shirin haihuwa

A baya NAIJ.com ta rahoto yadda ‘yar sarkin Kano ta halarci aurenta kamar wata sarauniya.

Fuskokin ma’auratan na dauke da farin ciki da annuri yayinda suka dauki hotuna da abokansu wanda a lokaci guda kuma dukkansu na shirin zama iyaye.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel