‘Yan canji a Najeriya na son a samar da farashin bai-daya

‘Yan canji a Najeriya na son a samar da farashin bai-daya

- Kungiyar 'yan canji sun bukaci bankin CBN da ta samar da farashi bai-daya na kudaden waje

- Sun ce hakan zai taimaka matuka gurin farfado da tattalin arzikin kasar domin zai ja hankulan masu zuba hannun jari a kasar

Kungiyar masu canjin kudade a Najeriya sun bukaci babban Bankin kasa wato CBN da ta samar da farashin tsayayye na kudaden waje, wanda zai taimaka wajen karkato da hankulan masu zuba hannun jari a kasar.

Najeriya da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a Afrika na fama da matsalar farashin kudaden waje, inda farashin Mahajjata ya banbata da na masu zuwa yawon shakatawa ko kuma biyan kudin makaranta a waje, yayin da farashin sari ga masu lasisi ya banbata da na kasuwannin bayan fage.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda wani malamin musulunci ya daure dalibinsa da mari (HOTUNA)

Kungiyar ta masu canji sun ce, magance matsalar banbancin farashin na kudaden waje zai daga darajar Naira, wanda hakan zai yi matukar tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Sakataren Kungiyar Alhaji Tanimu Ibrahim ya ce rarrabuwar farashin kudaden zai yi tasiri ga farashin kayayyaki.

A cewarsa, farashin bai-daya tare da kara yawan dala a kasuwa zai taimaka wajen farfado da darajar Naira.

Masharhanta dai na ganin daukar matakin tantance darajar Naira na da tasiri sosai ga masu saka jari musamman daga kasashen waje domin dajarar Naira zai ba su kwarin guiwar shigowa kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel