An gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benue Suswam akan zargin almundahana

An gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benue Suswam akan zargin almundahana

- An sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam akan zargin laifuka 32 iri-iri

- An gabatar da shi ne a babban kotun tarayya da ke zaune a Abuja yau Litinin

- An gurfanar da shi tare da wasu guda biyu; Omadachi Oklobia da Jeneth Aluga

Wani tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam ya gurfana gaban babban kotun tarayya da ke zaune a Abuja bisa ga laifuffuka 32 da ke tattare da rashawa da almundahana.

An gurfanar da tsohon gwamnan ne tare da wasu guda 2 Omadachi Oklobia, tsoho kwamishanan kudi da Jeneth Aluga,tsohon akawun jihar Benue.

YANZU-YANZU: An gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benue Suswam akan zargin almundahana

tsohon gwamnan jihar Benue Suswam akan zargin almundahana

Ana zarginsu da da laifin karkatar da biliyoyin Naira na shirin SURE-P da aka baiwa jihar Benue.

Game da cewar jaridar Premium Times, sun karyata zargin da ake musu.

KU KARANTA: Ba dimokradiyya ake a Najeriya ba - Tinubu

Zaku tuna cewa jaridar NAIJ.com ta sanar muku da cewa hukumar DSS ta garkame tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam bayan an gano wasu makuda dukiya a gidansa da ke Abuja.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel