Fasto yayi hasashen mutuwar Fani Kayode, kamar yadda shima yayi hasashen mutuwar Buhari

Fasto yayi hasashen mutuwar Fani Kayode, kamar yadda shima yayi hasashen mutuwar Buhari

- Fasto yace tauraron Fani Kayode ya kusan dusashewa

- Kayode tsohon minista ne a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo

Wani fasto dan Najeriya amma mazaunin kasar Amurka, Fasto Moshood Ifayemiwo ya hango mutuwar wani dan adawan shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma tsohon minista, Fani Kayode.

Faston yace nan bada dadewa ba tauraruwar Kayode zata dusashe, kuma Kayoden ka iya mutuwa, kamar yadda Faston yace ya gano daga wasu karance karance da yayi a cikin littafin Bible.

KU KARANTA: Gagararran mai garkuwa da mutane, ‘Evans’ ya kai 'yan sanda maɓuwayrsa (HOTUNA)

NAIJ.com ta ruwaito Fasto Moshood yana fadin “Ban taba haduwa da Fani Kayode ba, amma na hangi halin da zai shiga a nan gaba, sai dai abin da na gani shine zai iya mutuwa nan bada dadewa ba, idan bai fara addu’a da kuma canza halayyarsa ba.” Inji Faston.

Fasto yayi hasashen mutuwar Fani Kayode, kamar yadda shima yayi hasashen mutuwar Buhari

Fasto Moshood da Fani Kayode

Fasto Moshood ya tubure, inda yace ruhi mai tsarku ne ya shaida masa halin da Kayode zai shiga.

Idan ba’a manta ba, a yan kwanakin nan ne Fani Kayode yayi has ashen mutuwar shugaba Buhari, inda yace bai ga dalilin da zai sa a cigaba da yin rufa rufa da rashin lafiyar Buhari ba, don haka ne yake ganin wata kila Buharin ya mutu ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel