An tsinci gawar dattijon jam'iyyar APC a rafi

An tsinci gawar dattijon jam'iyyar APC a rafi

- Gawar Olumide Odimayo jigo a jami'iyar APC a gefen rafi

- An dai sace Olumide Odimayo ne a ranar alhamis 15 ga watan yuli.

- An tsinci gawan ne a rafin Ogolo da ke tsakanin Sabomi da Egbotu da ke karamar hukumar Ese Odo da ke Jihar Ondo.

An tsinci gawar Jigo a jami'iyar APC daga jihar Ondo mai suna Olumide Odimayo wanda masu garkuwa da mutane suka sace kwanakin baya.

Kamar yadda manema labarai suka ruwaito, an tsince gawar nasa ne a gefen rafin Ogolo da ke tsakanin Sabomi da Egbotu da ke karamar hukumar Ese Odo da ke Jihar Ondo.

Rahoto ya nuna cewa wasu 'yan bindiga dadi ne suka shiga unguwar tasu suna harbe-harbe da bindigogi kuma suka tafi da shi.

An tsinci gawar dattijon jam'iyyar APC a rafi

An tsinci gawar dattijon jam'iyyar APC a rafi

Wata majiya ta sanar da manema labarai cewa an tsinta gawar ne bayan yan banga na unguwar sun dukufa wajen neman shi.

"Mun sami labarin mutuwan ne ta bakin daya daga cikin 'yan bangan da suka yi ta neman Marigayi Olumide, dan bangan yace sun tsince gawar ne a gefen rafin Ogolo da ke tsakanin Sabomi da Egbotu da ke karamar hukumar Ese Odo da ke Jihar Ondo.

"Muna juyayi da bakin cikin akan aukuwar wannan lamarin kuma domin bamu samu daman gano sa kafin ya mutu"

Wani saurayi a unguwar ya daura alhakin kisan akan sojojin ruwa da ke aiki a garin domin sun kasa gano shi kafin a kashe shi. Ya cigaba da cewa idan da sojojin ruwan da yan banga sun tsananta bincike kuma cikin gagawa, watakila da Olumide bai rasa ransa ba.

"Shi dai marigayin (Olumide) bai dade da dawowa daga birnin London ba kafin a sace shi. Mai yiwuwa ya mutu ne saboda damuwa da halin matsi da ya shiga."

Jami'in hulda da jama'a na APC reshen Ondo mai suna Omo'ba Abayomi Adesanya shima ya nuna juyayin sa ba bakin ciki akan lamarin. Yace marigayin ya dawo daga London ne tun ya ciga da yi ma jam'iya hidima.

Yace yan jami'yan suna ta aikawa da sakon ta'aziyar su ga iyalan marigayin.

Wata majiya ta ce yan bangan sun kama mutane biyu wanda ake zargi da hannu a cikin lamarin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel