Akalla mutane 3 sun hallaka a rikicin jihar Taraba

Akalla mutane 3 sun hallaka a rikicin jihar Taraba

- Wata rikicin kabila ya faru a Gembu, Nguroje da wasu sassan jihar Taraba

- Akalla an hallaka mutane 3 a rikicin kuma da yiwuwan karuwa

Rahotannin da suka shigo game da sabuwar rikicin da ta barke a jihar Taraba ya nuna cewa mutane 3 sun hallaka yanzu.

Game da cewar jaridar Premium Times, wannan hayaniya ya balla ne a a Gembu, Nguroje da wasu sassan karamar hukumar Sardauna.

Ana zargin cewa rikici ne tsakanin kabilar Kakas da Fulani.

Mazauna unguwannin sun bayyana cewa rikicin ya balle ne da safiyar ranan Lahadi yayinda wasu matasa suka fasa ka hanya suna lalata dukiyoyin mutane.

Akalla mutane 3 sun hallaka a rikicin jihar Taraba

Akalla mutane 3 sun hallaka a rikicin jihar Taraba

“A yanzu da nike muku Magana, rikici ta barke sun kawo mana hari kuma an kasha wasunmu” Wani mazauni ya bayyana hakan.

KU KARANTA: Al-Mustafa ya bayyana asalin abinda ya kashe Abacha

Yayinda ake tattara wannan labara, ba’a samu damar Magana da kakakin hukumar yan sanda jihar, David Misal ba. Amma wani majiyar hukumar ya bayyana cewa an kafa dokar ta baci a yankin kuma har yanzu ba’a iyakan mutanen da aka hallaka ba.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel