'Buhari ya daukaka addinin Islama, ya durkusar da Kiristanci'

'Buhari ya daukaka addinin Islama, ya durkusar da Kiristanci'

- Najeriya kasa ce mai bin addinai daban-daban

- Ana yawan zargin Buhari da fifita addininsa kan na wasu

- Reno Omkri yace an cire CRK ne daga makarantu don gallazawa Kirista

Tsohon hadimin tsohon shugaba Goodluck Jonathan a tsohuwar gwamnati ta jam'iyyar PDP, Reno Omokri, yayi zargin cewa shugaba Buhari nayi wa addinin Kiristanci makarkashiya don kambama nasa addinin.

A cewar sa, an cire karantarwar addinin Kirista daga makarantun Najeriya, an maye gurbinsu da na addinin Islama. A shafinsa na sada zumunta ta Facebook dai, Pasto Omokri, yayi shagube ga manyan limaman coci masu mara wa shugaba Buhari baya da cewa ai ga irinta nan, wai Buhari ya fifita nasa addini n bai cire koyarda Islama a makarantu ba.

'Buhari ya daukaka addinin Islama, ya durkusar da Kiristanci'

'Buhari ya daukaka addinin Islama, ya durkusar da Kiristanci'

Rev. father Mbaka dai, da Pastor Tunde Bakare, su yayi wa wannan caccaka, domin su ne suke ja gaba wajen tallata shugaba Buhari a wurin dumbin mabiyansu.

A dai rahotanni da ke fitowa daga shafukan sada zumunta, wadanda gwamnati bata musa ko tabbatar ba zuwa yanzu, shine wai an cire karatun CRK wato na kiristanci daga jaddawalin makarantun Boko, amma a'a cire IRK ba, wanda yake karantar da addinin Islama.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel