'A dare daya Sambo Dasuki ya kashe dala biliyan daya'

'A dare daya Sambo Dasuki ya kashe dala biliyan daya'

- Har yanzu ana tsare ana tsare da Col. Sambo Dasuki

- A dare daya kacal wai ya batar da biliyan ta dala

- Ya ki bayanin ina ya kai kudin

A ci gaba da tatsar bayanai da ake yi kan binciken badakalar makamai da ake zargin Sambo Dasuki da yi, gwamnati tace hadari ne sosai sakin nasa, saboda irin makudan kudaden da ya ki bayaninsu.

"A rana kawai Col. Sambo Dasuki yayi cefanen kusan rabin tiriliyan na naira, cikin dala, watau fiye da biliyan daya na dala, kuma duk matsa ya ki bayanin ina ya kai kudin, ko me aka yi da su, ko me ya saya dasu," inji gwamnatin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Abin al’ajabi: Wani masallaci da mata da maza ke ibada a tare

'A dare daya Sambo Dasuki ya kashe dala biliyan daya'

'A dare daya Sambo Dasuki ya kashe dala biliyan daya'

A bayanin kare kai ne dai Ministan yada labarai, Alh. Lai Muhammed ya ke wannan bayani, inda yace, ba wai kin bin umurnin kotu ne gwamnatinsu bata yi ba, a'a, hadarin da ke tattare da sakin nasu ne matsala.

A cewarsa, Ba yadda za'ayi a saki wanda ya kwashe kudi har tiriliyan ya boye, wannan zai iya hambaras da gwamnati in ya sami dama.'

Ya kuma kara da cewa, Sheikh El-Zakzaki yana gida a cikin iyalansa a nutse, wai ba za'a barshi da jama'a bane saboda sun ki jinin makwabtaka dashi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel