Sanata Shehu Sani ya zayyana abubuwa 10 da suka dabaibaye Najeriya

Sanata Shehu Sani ya zayyana abubuwa 10 da suka dabaibaye Najeriya

Sanata Shehu Sani dan rajin kare hakkin dan-adam ne mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattijai

Lokaci zuwa lokaci, Sanata Shehu Sani kan yi tsokaci kan harkokin siyasar kasa, tattalin arziki, da ma batun talakawa, musamman a jiharsa ta Kaduna, inda ake sa ran zai iya yin takarar kujerar gwamna.

Sanata Shehu Sani ya zayyana abubuwa 10 da suka dabaibaye Najeriya

Sanata Shehu Sani ya zayyana abubuwa 10 da suka dabaibaye Najeriya

Senata Shehu Sani ya lissafa abubuwa goma da suka dabaibaye Najeriya.

Senata Shehu Sani wanda ke wakiltan Kaduna ta tsakiya ya zayyano abubuwa guda goma da suka dabaibaye Najeriya kamar haka;

1. Dogaro da hanya daya tilo na samun kudin shiga daga bangare daya na kasar, wanda idan anyi nazari za’a a ga sauran bangarorin a matsayin cima zaune suke.

2. Rashin tunawa da darrusan da muka koya daga yakokin baya.

3. Son zuciya da rura wutar gaba da kiyyaya ta addini da kabilanci da yan siyasa ke yi.

4. Rashin kishin kasa a zukantan ‘yan Najeriya, ana iya gane hakan ta yadda jama’a suke nuna halin ko in kula a ranakun bukin samun ‘yancin kasa wato daya ga watan Octoba.

5. Yawan gwamnatocin da basu tabuka ma jama’a komai ba, tabarbarewan tattalin arziki da kuma yadda masu arkziki ke ma talakawa pintinkau.

6. Samari mara sa hakuri da hangen nesa, wanda kuma basu waiwayon tarihi don su kooy darasi.

7. Dogewa kan tsarin rabon arziki na kasa ba tare da lalubo sababib hanyoyin samar da arzikin ba

8. Rashin kulawa da tsare-tasaren gwamnati da ke kara kula dankon zumunci da hadin kai tsakanin ‘yan kasa misali Tsarin Hidmar kasa (NYSC) da kuma makarantun sakandiri na gwanmantin tarraya.

9. Ra’ayoyi mara sa amfani da kuma yunkurin jefa kiyyaya tsakanin mutanen Najeriya bisa ga Kabilanci da yunkurin balle wa daga Kasar.

10. Rashinn yalwar arziki tsakanin Jama’a, saidai wasu ‘yan tsiraru sukayi babakere suna cin kudin a yayin da mafi yawan jama’a suna cikin talauci mai zafi.

Daga bisani Senata Sani ya bada shawaran a kaffa committee wanda zata zauna ta tattauna akan kuka da wasu kungiyoyi daga sassan Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel