Babu wani abun arziki da ya faru a gwamnatin Buhari – Olu Falae

Babu wani abun arziki da ya faru a gwamnatin Buhari – Olu Falae

- Tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya Olu Falae ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin tsinana ma kasar komai tun bayan da yah au kujerar mulki a shekarar 2015

- Falae ya ce babu wani abun arziki da ya faru a karkashin gwamnatin shugaban kasa Buhari

- Ya kuma yi watsi da kasafin kudin 2017

Tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya Olu Falae ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin tsinana ma kasar komai tun bayan da yah au kujerar mulki a watan Mayun shekarar 2015 jaridar Vanguard ta ruwaito.

Falae ya ce babu wani abun arziki da ya faru a karkashin gwamnatin da shugaban kasa Buhari ke jagoranta.

Tsohon babban sakataren tarayyar ya ce rashin lafiyar Buhari ya hana sa aiwatar da ayyukan da suka rataya a wuyan sa a matsayin san a shugaban kasar Najeriya.

Babu wani abun arziki da ya faru a gwamnatin Buhari – Olu Falae

Babu wani abun arziki da ya faru a gwamnatin Buhari inji Olu Falae

Da yake tur da mika kasafin kudin 2017 a kurarren lokaci, Falae ya ce shugaban kasa Buhari ya gudanar da yawancin lokutan sa a matsayin shugaban kasa gurin rashin lafiya.

KU KARANTA KUMA: Manyan Arewa ne suka biya matasan Arewa don suyi barazana – Babafemi Ojudu

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa anyi amfani da wasu tsarurruka don ganin an ceto tattalin arzikin kasar dake durkushewa.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci masu hadimansa da minister da su gana da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kan duk wani abu da ya shafi aiki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel