A daina kidan gangan yaki – Inji Lai Mohammed

A daina kidan gangan yaki – Inji Lai Mohammed

- Ministan labarai da al’adu ya gargadi masu furta kalamai na kiyayya da su daina kidan gangan yaki a kasar

- Ministan ya bayyana damuwar sa a kan wasu mumunar kalamai da zai iya haddasa rabuwar kawuna

- Ministan ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da waɗanda suke tsunduma cikin jawabai na kiyayya

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya gargadi waɗanda ke ganguna na yaki ta hanyar jawabai na kiyayya cewa su nizanci irin wannan don samu hadin kai kasar.

Ministan ya bada wannan shawarwari ne a ranar Asabar, 17 ga watan Yuni a wani taron lacca "Lai Mohammed 10th Annual Ramadan Lecture" wanda aka gudanar a garin ministan, Oro da ke jihar Kwara.

Lai Mohammed ya bayyana damuwar sa a kan wasu mumunar kalamai da zai iya haddasa rabuwar kawuna da yaki a cikin kasar da wasu ke furtawa.

A daina kidan gangan yaki – Inji Lai Mohammed

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed

NAIJ.com ta ruwaito cewa ministan ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da waɗanda suke tsunduma cikin jawabai na kiyayya.

Ya ce: “Muna zaman lafiya da juna, kuma da yarda Allah zamu ci gaba da zanm lafiya saboda kasancewar mu tare zai iya kawo muna ci gaba.”

"Idan ana yaki a yau, babu wani daga cikinmu wanda zai tsere ko kai matasa ne ko tsoho, yaki bata san shekarun ka ba, haka kuma bata san ka kai Yoruba, Igbo ko Hausa ne." Inji ministan.

KU KARANTA: Ana wasan buya tsakanin wasu shugabanin arewa da jami'an tsaro

Cikin wadanda suka halarci lecca sun hada da sarakunan gargajiya daga jihar Kwara, ciki har da Oloro na Oro, Oba Abdulrauf Oyelaran, malamai addinnin musulmi da kirista, 'yan siyasa, dalibai da kuma mutane daga sauran fannin rayuwa daban-daban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana jerin nasarorin shugaba Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel