Ahmed Musa ya cancanci ayi alfahari da shi – Gwamnan jihar Kano

Ahmed Musa ya cancanci ayi alfahari da shi – Gwamnan jihar Kano

- Gwamnan jihar Kano ya yaba ma Ahmed Musa kan irin gudunmuwar da ya ba jihar

- Ya ce hakan ya tabbatar da cewa shin din dan halas ne bai manta alkhairin da ya samu daga kungiyar Kano Pillars ba

- Ya kuma bukaci sauran 'yan wasan Najeriya da suyi koyi dashi don kawo ci gaba a kasar

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yaba ma Musa kan abun arziki da ya yi ma al’umma, cikin abun da ya amfana, musamman daga Kano Pillars.

Ganduje wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar wasssani na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Galadima a gurin taron bude filin motsa jiki da jarumin kwallon kafar ya bude a jihar Kano, ya kara da cewa, “nayi matukar murna da farin ciki a kan wannan gini mai ban mamaki da Musa ya yi don ci gaban wasanni a jihar Kano da ma Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Yadda na tayar da Ahmed Musa ba tare da taimako ba – Mahaifiyarsa

“Ya zama dole ayi alfahari da Ahmed Musa. Ya bari mun yarda da cewa ‘yan wasan mu na bukatar zuba jari da zai taba rayukan sauran jama’a. wannan guri yana da matukar muhimmanci ga mutane da shekarunsu ya ja har ma da matasa don su kasance cikin koshin lafiya.

“Mun gode ma Ahmed Musa sannan kuma muna sa ran cewa irin wadannan gini ba zai kasance a Kano kawai ba. Muna bukatar shi da ma sauran ‘yan wasan Najeriya da suyi irin wannan jari a Kano, Arewa da Najeriya."

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis
NAIJ.com
Mailfire view pixel