Manyan Arewa ne suka biya matasan Arewa don suyi barazana – Babafemi Ojudu

Manyan Arewa ne suka biya matasan Arewa don suyi barazana – Babafemi Ojudu

- Babafemi Ojudu ya bukaci matasa da karda su bari wasu masu san zuciya suyi amfani da su

- Mataimaki ga shugaban kasar ya bayyan cewa matasa su yi fafutuka don a samu gwamnati mai kyau, ba wai don rabuwar kai da tashin hankali ba

- Ya bayyana cewa wasu masu tayar da kayar baya ne ke amfani da Biyafara a matsayin shiri na samun kudi

Sanata Babafemi Ojudu, wani mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan al’amuran siyasa, ya bayyana cewa wasu manyan arewa ne suke biyan matsan Arewa don sub a ‘yan kabilar Igbo dake zaune a yankin wa’adin barin yankin.

A cewar rahotanni, mataimaki ga shugaban kasar ya yi wannan sharhin ne a karshen mako yayinda ya wakilci mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo a gurin wani taro tare da shugabannin yankunan Arewa a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Najeriya daya! Hausawa sunyi shiga irin ta ‘yan kabilar Igbo don nuna kauna, bayan barazanar

NAIJ.com ta bayyana cewa ofishin mataimakin na musamman ga shugaban kasa a harkar matasa da al’amuran dalibai ne suka shirya taron.

Ya kuma bayyana cewa wasu masu tayar da kayar baya ne ke amfani da Biyafara a matsayin shiri na samun kudi.

A halin yanzu, NAIJ.com ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta janye kudirinta dake cewa a kama shugabannin kungiyoyin matasan Arewa da suka yi barazana ga ‘yan Igbo na su bar yankin, don gudun karda kamun na su ya haddasa rikici a yankin na arewa.

A yanzu an ce gwamnati na duba mataki da zai fi dacewa don kawo karshen al’amarin ta hanyar mayar da hankali ga tattaunawa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel