Masu fatutikar raba ballewa daga Najeriya su jira sai shekarar 2114 – Shugaban OPC

Masu fatutikar raba ballewa daga Najeriya su jira sai shekarar 2114 – Shugaban OPC

- Shugaban kungiyar ‘Oodua Peoples’ Congress (OPC)’ Dakta Frederick Fasheun, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke fafutikar a raba kasar da su jira sai shekarar 2114.

- Fasheun ya ce wannan shekara ita ce za ta fi dacewa da ballewar Nijeriya tunda a lokacin ne kasar ta cika Shekaru 200 da kafuwa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya ce har tunda Nijeriya ta iya kaiwa shekaru 100 (2014), toh ya kamata kowa ya yi hakuri a kara yin wasu 100, idan abubuwa sun ki, sai a yi batun rabuwa.

A cewar shi “A tunani na, babu wanda ya isa ya mayar da Nijeriya baya…”

Masu fatutikar raba ballewa daga Najeriya su jira sai shekarar 2114 – Shugaban OPC

Masu fatutikar raba ballewa daga Najeriya su jira sai shekarar 2114 – Shugaban OPC

“Da wuya a samu kasar da ba ta fuskantar tashe tashen hankulan da ke da alaka da banbance banbancen kabila. Ba a kan mu aka fara, hasali ma abunda ake tsammani kenan ga kasar da take bunkasa”

Game da shigar sa Jam’iyyar GPN, Fasheun ya ce ya yi haka me saboda jam’iyyar PDP da na APC sun riga sun mutu, wanda kuma ana bukatar wata jam’iyya da za ta shigo tsakani ta raba Nijeriya daga tarwatsewa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel