Masha'Allah! Musulunci ya samu karuwa a jihar Sokoto

Masha'Allah! Musulunci ya samu karuwa a jihar Sokoto

A yayin da aka tunkari kwanakin karshe na azumin watan Ramadan, inda ake gudanar da tafsiri da sharhi kan ayoyin Alkur’ani mai girma, a masallatai da wuraren karantarwa, domin koyar da darussan addini da rayuwa ta duniya da lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa, yayin gudanar da wadannan tafsirai an samu shigar wasu mutane cikin addinin Musulunci, wadanda a baya suka kasance masu bin koyarwar wani addini daban. Tare da bayyana kwadayin su na samun dimbin rabon da Musulmi ke samu.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a karo na biyu a masallacin Unguwar Koko dake birnin Sakkwato, an samu wani bawan Allah da ya musulunta a wajen tafsirin Ustaz Bashar Ahmad Sani, wanda ake yi a masallacin Aliyu bn Dalib.

Masha'Allah! Musulunci ya samu karuwa a jihar Sokoto

Masha'Allah! Musulunci ya samu karuwa a jihar Sokoto

A yanzu ana kiran wannan bawan Allah da suna Ibrahim, bayan ya zabi sunan.

Malamin ya yi bayanin akwai bukatar taimakawa wannan bawan Allah kasancewar shi, yana da iyali kuma ya baro garin da yake.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da Gwamnati da a samar da gidajen ajiye ire iren wadannan bayin Allah.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel