LABARI DA DUMI-DUMI: An kafa dokar hana fita a karamar hukumar Sardauna jihar Taraba

LABARI DA DUMI-DUMI: An kafa dokar hana fita a karamar hukumar Sardauna jihar Taraba

- Gwamnatin jihar Taraba ta kafa dokar hana fita a yankin Mambila da Nguroje da ke karamar hukumar Sardauna

- Rahotanni na cewa wani dan siyasa a yankin ne yaje ya tunzura wasu matasa don tada zauna tsaye

- An kafa dokar hana fita a wasu yankunan da lamarin ya auku baya ga tura karin jami’an tsaro da suka hada da sojoji

Wannan sabon tashin hankali ya auku ne biyo bayan yunkurin da wasu matasan kabilar Mambila suka yi na hana jami’an tsaron farin kaya cafke wasu da ake zargin suna da hannu a tashe tashen hankula dake aukuwa a yankin.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, rahotanni na cewa wani dan siyasa a yankin ne yaje ya tunzura wasu matasa dake kusa da Nguroje don su hana kamun, kuma ganin basu samu sa’a ba, sai kawai suka shiga fashe fashe da kona taya har zuwa Gembu dake zama hedikwatar karamar hukumar Sardaunan.

Koda yake hukumomin tsaro basu tabbatar da batun asarar rayuka ba, wasu mazauna yankin da rikicin ya rutsa dasu sun bayyana cewa an kona gidaje baya ga rayukan da aka rasa ciki harda na dabbobi.

LABARI DA DUMI-DUMI: An kafa dokar hana fita a karamar hukumar Sardauna jihar Taraba

Jami'an tsaro a karamar hukumar Sardauna ta jihar Taraba

KU KARANTA: Dakarun Soji sun ragargaji mayaƙan Boko Haram, sun kashe 13

Wasu mazauna yankin da rikicin ya ratsu dasu, sun bayyana hali da ake ciki da kuma iri hasarar da aka yi.

Inji wani mazaunan yankin: “Mutane a Mambila ne da Ngurori mutane sun yi ta gudu sai kuma wasu su ka zo domin su kwashe kayan su, aka yi ta kona gidan mutane. Shi kuma daya mutumin cewa yayi gaskiya a yankin mu abin ba kyau, wallahi ana kone gidajen mutane kuma an kashe wasu.’’

Tuni aka kafa dokar hana fita a wasu yankunan da lamarin ya auku baya ga tura karin jami’an tsaro da suka hada da sojoji kamar yadda ASP David Misal, kakakin rundunan yan sandan jihar Taraban ya tabbatar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda wasu kabilar Yarabawa suka kare Hausawa mazaunan garin ILe-Ife a rikicin kabilancin da ta auku

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel