Osinbajo ya caccaki jiga-jigan yan siyasan Najeriya

Osinbajo ya caccaki jiga-jigan yan siyasan Najeriya

- Osinbajo ya ce wasu gurbatattun 'yan siyasa ne ke tunzura matasan kudu da arewa don haddasa rikici a kasar nan

- Osinbajo ya jaddada cewa duk matashin da aka kama da furta kalaman tada tarzoma zai fuskanci shari’a

- Mukaddashin shugaban kasa ya bukaci matasan kasar nan su kauce wa gurbatattun shugabannin da kuma ‘yan siyasa domin zaman lafiya

- Nasiru Adhama ya ce ofishinsa zata gudanar da wani babban taro na matasa daga dukkan jihohin tarayya don tattauna kalubalen da ke fuskantar matasan

Mukaddashin shugaban kasar, Yemi Osinbajo a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni ya daganta tashin hankali da rikicin kabilanci a kasar cewa aikin hannun wasu bata garin ‘yan siyasa ne.

Osinbajo ya ce: “Wasu gurbatattun 'yan siyasa ne ke tunzura matasan kudu da arewa don haddasa rikici a kasar nan.”

Mukaddashin shugaban kasan ya kara da cewa duk matashi daga na kudu da arewa da aka kama da furta kalaman tada tarzoma zai fuskanci hukuncin zaman gidan kaso.

Osinbajo ya caccaki jiga-jigan yan siyasan Najeriya

Mukaddashin shugaban kasan, Farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci matasan kasar nan su kauce wa wasu gurbatattun shugabannin

KU KARANTA: Ka ji abin da Osinbajo ya fadawa Fastoci a cocin fadar shugaban kasa

NAIJ.com ta ruwaito cewa Osinbajo ya sanar da hakan ne a wani taron shuwagabannin matasan yankunan kasar wanda ofishin mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan matasa da kuma harkokin ‘yan makaranta ta shirya a NICON Transcorp da ke birnin Abuja.

Osinbajo, wanda Babafemi Ojudu, mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa ya wakilta, ya bukaci matasan kasar nan su kauce wa wasu gurbatattun shugabannin da kuma ‘yan siyasa domin zaman lafiya da kuma ci gaban kasar.

Mukaddashin shugaban kasan, Farfesa Yemi Osinbajo ya lura da cewa burin wadannan mutanen shine amfani da matasan zuwa ga cimma burin su na siyasa.

Mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan matasa da kuma harkokin ‘yan makaranta, Mista Nasiru Adhama bayyana cewa nan gaba ofishinsa zata gudanar da wani babban taro na matasa daga dukkan jihohin tarayya don tattauna kalubale da ke fuskantar matasa a kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Cikakken bayanin mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kan yakin basasan Najeriya a cikin wannan bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel