Yadda na tayar da Ahmed Musa ba tare da taimako ba – Mahaifiyarsa

Yadda na tayar da Ahmed Musa ba tare da taimako ba – Mahaifiyarsa

- Mahaifiyar Ahmed Musa ta ce ta raine shi tare da kannensa guda hudu ba tare da taimakon wani ba tun bayan rasuwar mahaifin sa

- Ta bayyana hakan ne a wani hira da akayi da ita a gurin taron bude filin wasan da jarumin na Super Eagles ya bude a jihar Kano

- Ta nuna Ahmed a matsayin sanyin idaniyan su

Mahaifiyar Ahmed Musa dan wasan kungiyar Super Eagles, Sarah Moses ta bayyana cewa ita kadai ta raini Ahmed da sauran ‘ya’yanta guda hudu bayan rasuwar mijinta shekaru 20 da suka wuce.

Da ake hira da ita, mahaifiyar Musa mai shekaru sittin wacce ta halarci taron bude filin motsa jiki na naira miliyan 500 da danta ya gina a Kano ta bayyana Musa a matsayin shuni wanda ya taba rayukan mutane da dama da dukiyarsa, musamman, matan da mazajensu suka rasu da kuma marayu, ta kara da cewa “ya kansance sanyin idaniyan mu dama na ‘yan ubansa. Yana kula damu baki daya.”

KU KARANTA KUMA: Rikicin siyasa: APC ta dakatar da wasu daga cikin mambobin ta

Yadda na tayar da Ahmed Musa ba tare da taimako ba – Mahaifiyarsa

Mahaifiyar Amed Musa ta ce ita kadai ta raine shi ba tare da taimakon kowa ba bayan rasuwar mahaifin sa

A cewar ta, sabanin cewa da akeyi Ahmed ya fito daga Jos, jihar Plateau, mahaifiyarsa ta ce: “a zahirin gaskiya ya fito ne daga Maiduguri a jihar Borno. Nice ta biyu a gurin mahaifinsa wanda ya rasu Musa na da shekaru bakwai a lokacin.

“Ni mabiyar addinin Kirista ce daga jihar Edo sannan kuma mahaifin Musa musulmi ne, wannan ne dalilin da yasa nake amfani da suna Moses. Mahaifinsa ya kasance mutun mai kula da karamci; mutumin kirki wanda ya kula da dukkan matan sa kafin rasuwarsa. Ina matukar farin ciki ganin ana karrama abun da na haifa a tsakanin manya da yara. Don haka, ina godiya ga Allah kuma burina ya cika.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel