Dalilin da yasa miyagun ayyuka kamar su fashi da fyaɗe ke ƙaruwa – Ɗansanda

Dalilin da yasa miyagun ayyuka kamar su fashi da fyaɗe ke ƙaruwa – Ɗansanda

- Yansanda sun bayyana dalilin karuwar munanan ayyuka a kasa

- Yansandan sun danganta ayyukan da kungiyar asiri

Rundunar yansandan jihar Enugu ta bayyana musabbabin kara yaduwar miyagun ayyuka a tsakanin al’umma, inda rundunar ta danganta hakan da ayyukan matasa yan kungiyar asiri.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito, Kaakakin rundunar Ebere Amaraizu ya bayyana cewa sun dauki matakin zagaya dukkanin makarantun sakandari da na gaba da sakandari da kuma tashoshin mota domin wayar da kawunan jama’a game da miyagun ayyuka.

KU KARANTA: Taƙaddama ta ɓarke tsakanin Sanatoci da shugaban hukumar Hajj ta ƙasa (Hotuna/Bidiyo)

“Aikin kungiyar asiri mummunar lamari ne, shike sanya matasa aikata fyade, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.” Inji shi.

Dalilin da yasa miyagun ayyuka kamar su fashi da fyaɗe ke ƙaruwa – Ɗansanda

Matsan kungiyoyin asiri da aka kama a baya

Kakkaki Ebere ya kara da cewa ayyukan kungiyoyin matsafa na lalata rayuwar matasan da suka kusance ta, don haka ne ya gargadi matasa da su hankalta, kua su zamo masu bin doka da da’a, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

“Ayyukan kungiyar matsafa sun fadada har zuwa kan yan kasuwa, direbobin mota, mahauta da sauran matasa da dama, don haka ya zama dole matasa su san wanene abokinsu, da sana’arsu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana yi ma wani sanata kiranye

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel