Boko Haram: An karkatar da rabin abincin 'yan gudun hijira

Boko Haram: An karkatar da rabin abincin 'yan gudun hijira

- Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa kusan rabin abincin ‘yan gudun hijira ne aka karkata a jihar Borno

- Wani sabon tsarin da gwamnati ta bullo da shi ya taimaka sosai wajen rage karkatar da kayan abincin

- A yanzu fiye da mutanen miliyan 1.5 ke fuskantar barazanar bala'in yunwa a sansannin ‘yan gudun hijiran

Jami'ai a Najeriya sun ce rabin kayan abincin da gwamnati ta aika da su don taimakawa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa, ba su shiga hannun mutanen ba.

Mai magana da yawun mukaddashin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce sabon tsarin da aka bullo da shi a farkon wannan watan, ya taimaka sosai wajen rage karkatar da kayan abincin.

Ya ce yanzu, daruruwan sojoji da 'yan sanda ne ke yi wa kayan abincin rakiya a arewa maso gabashin kasar.

Boko Haram: An karkatar da rabin abincin 'yan gudun hijira

Kayan abinci da aka kai sansanin 'yan gudun hijira da ke Bama a jihar Borno

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, kimanin mutum miliyan 3 ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin na Boko Haram a tsawon shekaru takwas.

Wasu mutanen miliyan 1.5 kuma na fuskantar barazanar bala'in yunwa.

KU KARANTA: Labari da dumi-dumi: Farashin mai ya ragu a Najeriya – NNPC

In ba a manta ba, a farkon watan nan ne mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, yayin da yake kaddamar da wata sabon shirin gwamnatin tarayya a Maiduguri babban birnin jihar Borno, ya ce ‘yan gudun hijira zasu daina yi jerin gwano domin abinci, ya ce yanzu haka za a kai masu har bankin kofar su.

Mayakan kungiyar ta Boko Haram na ci gaba da kai hare-haren ta’addanci, duk da galabaitar da su da sojojin kasar suka ce sun yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zanga-zangar 'yan fafutukutar kafa yankin Biyafara a birnin Abuja

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel