An kai harin ta’addanci a kusa da wani masallaci da ke Landan (Hotuna)

An kai harin ta’addanci a kusa da wani masallaci da ke Landan (Hotuna)

- Wata babbar mota ta kai hari kan mutanen da ke tafiya a kasa a kusa da masallacin Finsbury Park da ke arewacin Landan

- Yanzu jami’an tsaro sun tsare mutum daya dangane da harin motar ta kutsa kai a kan mutanen da ke tafiya a kusa da masallacin Finsbury Park

- Theresa May ta yi Allah wadai da harin, a cewar ta wannan mummunan al'amari ne

Mutane da dama ne suka jikkata bayan wata babbar mota ta bi ta kan mutanen da ke tafiya a kasa a kusa da masallacin Finsbury Park da ke arewacin Landan, a abin da 'yan sanda suka bayyana a matsayin "babban lamari".

An tsare mutum daya bayan motar ta kutsa kai a kan mutanen da ke tafiya a kusa da masallacin, wanda ke kusa da kan titin Seven Sisters.

An kira jami'an tsaro da misalin karfe 12:20 na tsakar dare kuma har yanzu suna can, a cewar rundunar 'yan sandan birnin.

An kai harin ta’addanci a kusa da wani masallaci da ke Landan (Hotuna)

An kai harin ta’addanci a kusa da wani masallaci da ke Landan (Hotuna)

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Majalisar Musulmin Birtaniya ta ce da gangan babbar motar ta fada kan masu ibada.

An yi amannar cewa akasarin mutanen da lamarin ya rutsa da su sun kammala sallar Isha'i ne bayan sun sha ruwa a lokacin da suke kan hanyarsu zuwa gida.

An kai harin ta’addanci a kusa da wani masallaci da ke Landan (Hotuna)

Masallacin Finsbury Park na kusa da titin Seven Sisters

Hukumar kwana-kwana ta birnin Landan ta ce ta aika da ma'aikatanta da dama zuwa wurin.

Tuni jami'an tsaro suka killace wurin.

An kai harin ta’addanci a kusa da wani masallaci da ke Landan (Hotuna)

Jami'an 'yan sandan birnin Landan

Wani bidiyo da aka wallafa kan yadda lamarin ya faru ya nuna yadda mutane suka fada cikin rudani a lokacin da ake kokarin taimakawa wadanda suka ji rauni.

An kai harin ta’addanci a kusa da wani masallaci da ke Landan (Hotuna)

Harin ta’addanci a kusa da wani masallaci da ke birnin Landan

An ga wani mutum yana taimakawa wani mutumi da ya jikkata a kan titi yayin da aka ga wani kuma yana yi wa wani wanda ya samu rauni a kansa magani.

Wani ganau yace ya kauce daga kan hanya a lokacin da motar ta kai harin.

Ya kara da cewa: "Mutumin da ke cikin motar ya far mana babu zato babu tsammani. Akwai mutane da dama. An gaya mana mu rika tafiya ba tare da mun kace daga hanya ba. Na yi matukar kaduwa."

Firai Ministar Burtaniya Theresa May ta bayyana harin da cewa: "Wannan mummunan al'amari ne. Ina mika jajena ga mutanen da suka jikkata da 'yan uwansu da kuma masu bayar da agajin gaggawa da suka je wurin".

KU KARANTA: An sake kama wata bisa zargin garkuwa da mutane

Shi ma jagoran jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn, wanda yake zaune a kusa da wurin da lamarin ya faru, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Na yi matukar kaduwa da jin labarin harin da aka kai Finsbury Park a dare Lahadi, 18 ga watan Yuni. Na yi magana da masallatai da 'yan sanda da kuma hukumar yankin Islington a kan wannan lamari. Ina mika jajena ga al'umar da wannan ibtila'i ya shafa".

Magajin birnin London Sadiq Khan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa jami'an bayar da agajin gaggawa sun je wurin da lamarin ya faru kuma ana gudanar da bincike kan batun.

Mohammed Shafiq na gidauniyar Ramadhan Foundation, wata kungiyar Musulmi da ke yaki da masu tsattsauran ra'ayi, ya bayyana harin a matsayin "rashin hankali da shaidanci".

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin kudancin jihar Kaduna kashi na biyu a cikin wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel