Yansanda sun cika hannu da masu garkuwa da mutane a Kaduna su 6

Yansanda sun cika hannu da masu garkuwa da mutane a Kaduna su 6

- Yansandan jihar Kaduna sun kama masu garkuwa da mutane su shidda

- Yansandan sun kama su ne a wurare daban daban na jihar

Jami’an Yansanda dake aiki karkashin hukumar tsaro ta Operation yaki ta bayyana samun nasarar cafke wasu gawurtattun masu garkuwa da mutane akan titin Abuja zuwa Kaduna, su shidda.

A ranakun Alhamis 15 da Juma’a 16 ga watan Yuni ne jami’an tsaro suka kama wadannan miyagun mutane tare da hadin gwiwar runduna ta musamman daga ofishin babban hafsan yansanda.

KU KARANTA: Shari’ar Zakzaky ta fuskanci cikas a Kaduna

Mutanen da aka kama sun hada da: Adamu Mamman, Ali Rabo, Auwalu Ahmad, Shehu Idris Shagari, Umar Antijo da kuma Babangida Abdullahi wanda shike yi ma gungun ajiyar kayayyakin su.

Yansanda sun cika hannu da masu garkuwa da mutane a Kaduna su 6

Masu garkuwa da mutane a Kaduna su 6

Dayake bada sanarwar, shugaban rundunar Operation Yaki, Yakubu Yusuk, yace jihar Kaduna ce ke samar da kudin yaki da masu garkuwa da mutanen, inda ya kara da cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ba su dukkanin goyon bayan daya dace.

NAIJ.com ta ruwaito cewar miyagun mutanen sun watsu ne a sassan jihar, inda aka kakkamasu a yankuna daban daban da suka hada da Maraban Jos, Ungwan Pama, Sabon Gayan da kauyen Rijana, kuma dukkaninsu sun amsa laifukansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda yansanda suka yi da wnai gagare

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel