Labari da dumi-dumi: Farashin mai ya ragu a Najeriya – NNPC

Labari da dumi-dumi: Farashin mai ya ragu a Najeriya – NNPC

– Kamfanin man NNPC ya rage farashin man dizal da kaso mai tsoka

– Ana saida lita a kan kusan N300 wanda yanzu yayi kasa da N200

– Mai magana da bakin Kamfanin ya bayyana wannan cigaba da aka samu

Farashin man dizal ya ragu yanzu a Najeriya Inji kamfanin NNPC. An samu saukin kusan kashi 42 bisa 100 kan abin da ake saidawa a baya. Jama’a dai za su ji dadin wannan sauki da aka samu a fadin kasar.

Labari da dumi-dumi: Farashin mai ya ragu a Najeriya – NNPC

Kamfanin NNPC ya rage farashin man dizal zuwa N175

Masu motoci da Injin da ke amfani da man dizal za su yi murnar yadda aka rage kudin man daga N300 zuwa N175. Farashin litan man ba zai dai wuce N200 ba daga yanzu kamar yadda kamfanin NNPC ya bayyana.

KU KARANTA: Muna cikin mugun hali Inji Hausawan da ke Kudu

Labari da dumi-dumi: Farashin mai ya ragu a Najeriya – NNPC

Shugaban Kamfanin man kasa NNPC

Mai magana da bakin Kamfanin watau Udu Ughamadu ya bayyana wannan cigaba da aka samu jiya inda ya ke jawabin irin matakan da su ka dauka domin saumun sauki da arahar kayan a cikin kasar.

Ku na da labari cewa takin da Gwamnatin Tarayya ke saidawa ya fara tsada. A wasu wuraren ma dai an fara boye takin na zamani. Manoma dai sun koka da yadda kudin takin ya tsula daga N5500 zuwa N6500 kwanan nan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mutum yayi kudi da garkuwa da mutane

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel