Dakarun Soji sun ragargaji mayaƙan Boko Haram, sun kashe 13

Dakarun Soji sun ragargaji mayaƙan Boko Haram, sun kashe 13

- Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram goma sha uku

- An kashe maharan ne a kauyen Gumsuri yayin da suka kai hari

Wasu rahotanni da suka ishe gidan rediyon BBC Hausa sun bayyana yadda aka kai ruwa rana tsakanin dakarun Sojin kasar nan da mayakan Boko Haram a kauyen Gumsuri dake jihar Borno.

Wani shaidan gani da ido da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida ma majiyar NAIJ.com cewar Sojojin sun hallaka yan Boko Haramun ne yayin wata bata kashi da sukayi, inda aka gwabza a kauyen Gumsuri a lokacin da yan ta’addan suka kai hari kauyen.

KU KARANTA: Kalli yadda aka dambace a majalisar jihar Nassarawa (Bidiyo)

“Da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Asabar ne yan Boko Haram suka kawo harin, sai dai Sojoji sun kawo mana dauki, tare da yan Sibiliyan JTF, inda aka kashe yan Boko Haram 13, kuma aka kwace makamai 13 tare da awakai da dama.” Kamar yadda ganau din ya bayyana.

Dakarun Soji ragargaji mayaƙan Boko Haram, sun kashe 13

Dakarun Soji

A cewar shaidar gani da idon, mutanen kauyen su biyu sun rasu sakamakon harin. Haka zalika Kaakakin rundunar Sojin kasa Birgediya SK Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace gawawwakin yan Boko Haram 10 kadai suka iske.

Sai dai SK Usman ya musanta labarin cewa wasu mutanen kauyen Gumusri sun mutu, inda yace babu wani soja ko dan garin da yayi asarar rayuwarsa, ko ya ji rauni.

Wasu rahotanni sun bayyana cewar yan Boko Haram suna kai hari kauyukan yankunan ne domin satar abinci da dabbobi, sakamakon an dates duk wasu hanyoyin da suke samun abinci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sojojin sama suna kashe yan Boko Haram, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel