Harin ƙunar bakin wake yayi sanadiyyar mutuwar mutane 8 a Maiduguri

Harin ƙunar bakin wake yayi sanadiyyar mutuwar mutane 8 a Maiduguri

- Yan kunar bakin wake sun kai hari kusa da sansanin yan gudun Hijira

- Akalla mutane 30 sun jikkata sakamakon harin

Maharan Boko Haram yan kunar bakin wake dauke da jigidar bom sun kai wata mummunar hari a sansanin yan gudun hijira dake Kofa, gab da sansanin yan gudun hijra dake Dalori.

Kimanin mutane 8 ne suka riga mu gidan gaskiya, yayin da 30 kuma suka jikkata a sakamakon harin da yan kunar bakin waken su 3 suka kai.

KU KARANTA: Mata ta na jibga ta a duk lokacin da ta ji sha’awan yin haka – Inji Mijin tace

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace yan kunar bakin waken sun kai harin ne da misalin karfe 8:45 na daren ranar Lahadi 18 ga watan Yuni.

Harin ƙunar bakin wake yayi sanadiyyar mutuwar mutane 8 a Maiduguri

Harin ƙunar bakin wake

Wata majiya mai tushe ta shaida ma jaridar Sahara Reporters cewar daya daga cikin yan kunar bakin waken ya tada bom din nasa ne a kusa da gidan dakacin Kofa, yayin da shi kuma daya ya tada nasa bom din kusa da wani Masallaci.

An hangi motoci cike da Sojoji yayin da suka nufi garin Dalori don taimaka ma Sojoji dake wajen.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Harin Sojoji akan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel