Gwamnati ta ce zata daukaka kara kan wanke shugaban majalisar dattijai

Gwamnati ta ce zata daukaka kara kan wanke shugaban majalisar dattijai

- Gwamnatin tarayya Najeriya ta ce zata daukaka kara kan wanke shugaban majalisar dattijai da kotun da’a ta yi

- Obono Obla, wanda ya lashi takobin cewa babu wani mai laifin cin hanci da rashawa da gwamnati zata bari

- Kotun da’a ta kasar ta wanke sanata Bukola Saraki kan zargi na kin bayyana dukiya ko kadaroinsa

A makon nan ne kotun da’a wacce take sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar kan shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki na kin bayyana dukiya ko kadaroinsa ta wanke shi.

Mataimaki shugaban kasa a kan gurfanar da masu laifi, Mista Okoi Obono-Obla, ya ce a ranar Asabar, 17 ga watan Yuni cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar daukaka kara kan hukuncin da kotun da’a ta yi a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni inda ta wanku shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a kan rashin bayyana dukiya ko kadaroinsa.

KU KARANTA: Kashin Alkalin da ya saki Shugaban Majalisa Bukola Saraki ya bushe

Gwamnati ta ce zata daukaka kara kan wanke shugaban majalisar dattijai

Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Obono-Obla ya lashi takobin cewa babu wani mai laifin cin hanci da rashawa da gwamnati zata bari ba tare da an hukunta shi ba, ya ce a cikin wata hira tarho cewa, gwamnati zata daukaka kara kan hukunci na ranar Laraba da ta gabata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel