Zaben 2019: Ba za mu baiwa Buhari tikitin takara kai tsaye a zaben 2019 – Inji jam’iyyar APC

Zaben 2019: Ba za mu baiwa Buhari tikitin takara kai tsaye a zaben 2019 – Inji jam’iyyar APC

- Shugaban jam’iyyar APC ta reshen arewa maso yamma ya ce shugaba Buhari ba zai samu tikitin takara kai tsaye a 2019 ba

- Alhaji Inuwa Abdulkadir ya ce idan shugaba Buhari ya tsallake zaben fidda gwani shike nan

- Jam'iyyar tace kofa a bude take ga duk mai sha'war tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019

Jama'iyyar mai mulki APC ta ce, shugaba Muhammadu Buhari ba zai samu tikitin takara a zabukan 2019 kai tsaye ba.

Shugaban jam’iyyar APC ta reshen arewa maso yammacin kasar, Alhaji Inuwa Abdulkadir ya bayyana cewa jam’iyya ba zata baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari tikitin takara kai tsaye ba. Amma kuma idan ya tsallake zaben fidda gwani shike nan.

Jam'iyyar APC tace kofa a bude take ga duk mai sha'war tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019 domin ba zata baiwa Buhari kai tsaye ba.

Zaben 2019: Ba za mu baiwa Buhari tikitin takara kai tsaye a zaben 2019 – Inji jam’iyyar APC

Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin yakin neman zaben 2015

Mista Inuwa ya ce APC jam'iyyace ta kowa mai kokarin kwatanta adalci da dimokardiyya a cikinta. Saboda haka babu batun baiwa Buhari tikitin takara kai tsaye sai ya bi matakai na tsayawa takara.

KU KARANTA: Kashin Alkalin da ya saki Shugaban Majalisa Bukola Saraki ya bushe

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Inuwa na cewa idan shugaba Buhari na burin zarcewa a 2019 wajibi ne a gareshi ya tsayawa takara ya fafata shima a zaben fitar da gwamni. Idan ya tsallake shikenan idan kuma yasha kayi shikenan amma jam'iyyar ba zata bashi tikitin takara kai tsaye ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani jami'in jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel