Ana wasan buya tsakanin wasu shugabanin arewa da jami'an tsaro

Ana wasan buya tsakanin wasu shugabanin arewa da jami'an tsaro

- Har yanzu jami'an tsaro a jihar Kaduna basu samu nasarar kama shuwagabannin kungiyoyin arewa da suka fitar da sanarwar gargadi ga yan kabilar Ibo

- Rahotanni na nuna cewa wasu daga cikin shuwagabannin kungiyoyin arewa sun tsere daga jihar wasu kuma sun daina fitowa

- Gwamnan jihar Kaduna ya umurci hukumomin tsaro su gaggauta kama matasan da suka fitar da sanarwar gargadi ga yan kabilar Ibo

Rahotanni daga jihar Kaduna na nuna cewa har yanzu jami'an tsaro basu samu nasarar kama shuwagabannin kungiyoyin arewan nan da suka fitar da sanarwar gargadi ga yan kabilar Ibo a kwanakin baya.

Idan dai ba'a manta ba a kwanakin baya ne wasu gamayyar shuwagabannin kungiyoyin arewa suka hadu a Arewa House Kaduna inda sukayi taron manema labarai suna gargadin yan kabilar ibo dake yankin arewa da su tattara nasu inasu su fice daga arewa.

Kungiyoyin da suka sanya hannu a sanarwar sun hada da, Nastura Ashir Sharif, Arewa Citizens Action For Change; Amb. ShettimaYerima, Arewa Youth Consultative Forum; Aminu Adam, Arewa Youth Development Foundation: Alfred Solomon, Arewa Students Forum; Abdul-Azeez Suleiman, Northern Emancipation Network; Joshua Viashman, Northern Youth Vanguard, Mohammad A. Mohammad, Northern Youth Stakeholders Forum; Mohammed Tasiu Pantami, North East Assembly da kuma Nathaniel Ajegena Adigizi, North Central Peoples Front.

Ana wasan buya tsakanin wasu shugabanin arewa da jami'an tsaro

Shugabanin arewacin Najeriya

Sai dai kasa da kwana guda da fitar da sanarwar ne gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya umurci hukumomin tsaro su gaggauta kama matasan da suka fitar da sanarwar.

Tun bayan wannan umurni da gwamnan ya bayar duka matasan suka buya. A yayinda wasu kuma daga cikinsu suka fice daga jihar zuwa wasu jihohi.

KU KARANTA: 2019: Ikon Allah: Har da Patience Jonathan za a tsaya takara mai zuwa

Kamar yadda NAIJ.com ta samu daga shafin Hausa Times, Kakakin gamayyar kungiyoyin, Abdulazeez Suleiman, ya ce dama mafi yawan shuwagabannin kungiyoyin ba mazauna Kaduna bane. Hakan yasa duk sun fice daga jihar tare da boyewa don gudun tozarci.

Bayanai sunce wasu daga cikin matasan sun tsere makwaftan jihohi kamar Abuja, Kano da Fatakwal wasu kuma sun daina zirga zirga don gudun kamu.

Bayanai sunce tuni jami'an tsaro suka kafa shingayen bincike a hanyoyin Kaduna don cika wannan umurni na kama matasan amma har yanzu hakarsu bata cimma ruwa ba.

A yayinda wasu ke Allah wadai da wannan lamarin wasu kuma na ganin matasan arewan sunyi daidai

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Cikakken bayanin mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kan yakin basasan Najeriya a cikin wannan bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel