Kashin Alkalin da ya saki Shugaban Majalisa Bukola Saraki ya bushe

Kashin Alkalin da ya saki Shugaban Majalisa Bukola Saraki ya bushe

– Alkalin da ya wanke Shugaban Majalisar Dattawa ya shiga uku

– Hukumar EFCC na shirin taso Alkali Danladi Umaru a gaba

– Ana zargin Alkalin da karbar cin hanci daga Bukola Saraki

Alkali Danladi Umaru da ya wanke Saraki zai ga ta kan sa. EFCC za ta binciki lamarin inda ake zargin sa da karbar rashawa. An wanke Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki daga duk wani laifi.

Kashin Alkalin da ya saki Shugaban Majalisa Bukola Saraki ya bushe

Alkali ya wanke Shugaban Majalisar Dattawa Saraki

Alkalin Kotun CCT mai lura da kadarorin Jami’an Gwamnati Danladi Umaru da ya wanke Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dr. Bukola Saraki zai ga uwar-bari yayin da EFCC mai yaki da zamba ke shirin damke sa bisa zargin karban cin hanci.

KU KARANTA: Ka ji abin da Gwamnan Jihar Kaduna yayi

Kashin Alkalin da ya saki Shugaban Majalisa Bukola Saraki ya bushe

Alkalin da ya saki Bukola Saraki zai shiga hannun EFCC

Ana zargi Alkali Danladi Umar ya karbi rashawa na Naira Miliyan 10 ta hannun wani Alhaji Abdullahi Gambo wanda ke cikin yaran sa. An dai wanke Shugaban Majalisun Kasar Bukola Saraki daga duk wani laifi duk da karfin hujjoji.

Wani tsohon Mataimakin Shugaban Lauyoyin Najeriya watau NBA Monday Ubani yayi tir da nasarar da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya samu a Kotu inda yace Najeriya ce za tayi kuka ba kowa ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kasafin kudi: Ra'ayin 'Yan Najeriya [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel