Harkar noma: Takin Buhari ya kara farashi a kasuwa

Harkar noma: Takin Buhari ya kara farashi a kasuwa

– Takin Gwamnatin Buhari ya kara farashi a kasuwa

– Akwai rade-radin cewa Gwamnoni su ka sa takin ya tashi

– Yanzu haka dai takin ya kara kudi a kasuwa yayin da ake shirin aiki

Mu na da labari cewa takin da Gwamnati ke saidawa ya fara tsada. A wasu wuraren ma dai an fara boye takin na zamani . Manoma dai sun koka da yadda kudin takin ya tsula daga N5500 zuwa N6500.

Harkar noma: Takin Buhari ya kara farashi a kasuwa

Takin Buhari ya tsula daga N5500 zuwa N6500

NAIJ.com na da labari cewa takin da Gwamnatin Tarayya ke saidawa cikin rahusa ya fara tsada inda a wasu wuraren ma dai an fara boye takin na zamani a yanzu da manoma ke tsakiyar neman takin ido-rufe.

KU KARANTA: An kama masu garkuwa da mutane a Najeriya

Harkar noma: Takin Buhari ya kara farashi a kasuwa

Gwamnatin Tarayya na saida takin zamani cikin rahusa

Wani ‘Dan kasuwa ya bayyana cewa ba laifin su bane ya sa takin ya kara kudi ya ke cewa Gwamnoni ne su ka handame buhunan takin domin su rabawa ‘yan siyasa ko da dai cewa takin bai wani rage tsada a hannun su ba.

Kun dai ji cewa wani babban Jami’in CBN ke cewa tattalin arzikin Najeriya zai zabura zuwa karshen shekarar bana. Tsadar kaya na kara sauka, haka kuma dai ana samun sauki wajen canjin dala a halin yanzu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Har yanzu Najeriya ce kan-gaba a Afrika?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel