Yadda rikita rikitar aure na ta kawo mun matsala a kakar wasannin data gabata - Inji Ahmad Musa

Yadda rikita rikitar aure na ta kawo mun matsala a kakar wasannin data gabata - Inji Ahmad Musa

- Ahmad Musa dan wasan gaba na Super Eagle ya bayyana yadda sabon auren shi ya kawo masa matsala a kakar wasannin da ta gabata

- Kafin sabon Auren Musa ya saki tsohuwar matar shi wacce suka kwashe tsawon shekaru 4 da aure

- Ahmad Musa ya yi sabon Auren sa ne a kudancin kasar nan

Dan wasan gaba na Super Eagle dake Najeriya kuma mai taka leda kungiyar kwallon kafa ta Liecester City dake kasar Ingila Ahmad Musa ya bayyana yadda sabon Auren shi ya jawo mishi barazana a kakar wasannin da suka gabata.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Ahmad Musa ya ce kafin maganar sabon Auren shi ya taka rawar ganin sosai a kungiyar da yake taka leda, amma da maganar Auren ta taso gadan-gadan wasanni gagarar shi suka yi.

Sai dai yace wasannin da za'a fara a kaka ta gaba zai bada mamaki sosai.

Yadda rikita rikitar aure na ta kawo mun matsala a kakar wasannin data gabata -Ahmad Musa

Ahmad Musa dan wasan gaba na Super Eagle

Idan baku manta ba a baya bayan nan dan wasan Ahmad Musa ya yi sabon Aure a kudancin kasar nan mai suna Juliet.

KU KARANTA: Dalilin da yasa sarkin Kano ya kaiwa mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ziyara

Kafin Auren ya saki tsohuwar matar shi mai suna Jamila wacce suka kwashe tsawon shekaru 4 da ita bayan ta haifar mishi yara 2.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali wata 'yar motsa jiki, ta ce baiwa Allah ne

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel