Cin hancin miliyan 100 da Dangote ya baiwa ‘Yan majalisar Kano don dakatar da binciken Sarkin Kano ya jawo yamutsi

Cin hancin miliyan 100 da Dangote ya baiwa ‘Yan majalisar Kano don dakatar da binciken Sarkin Kano ya jawo yamutsi

Zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano ya yamutse sakamakon zargin rashin adalci da ‘ya’yan majalisar ke yi wa kakakin majalisar, Rayit Honarabul Kabiru Rurum wajen rabon naira miliyan 100 da Alhaji Aliko Dongote ya baiwa ‘yan majalisar don su dakatar da binciken da suke yi akan Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II bisa zarge-zargen kashe kudaden masarautar Kano ba bisa ka’ida ba da kuma wasu laifuka 7.

Jaridar Daily Nigerians ta rawaito daga majiya mai tushe cewa, Alhaji Aliko Dangote ya baiwa ‘yan majalisar Kano wuri na gugan wuri naira miliyan 100 donsu janye binciken da suke yi akan San Kano wanda ake zargi da yin facaka da kudaden masarautar Kano daadadinsu ya kai naira biliyan 4.

Ganin cewa ci gaba dabinciken ka iya sanyawa Sarkin ya rasa kujerarsa, ya sa Dangote da wasu manyan kasar nan suka shiga cikin maganar don tsarewa Sarki Muhammadu sanusi II mulkin sa.

In bamu manta ba dai a ranar 10 ga watan Mayu ne majalisar ta jihar Kano ta kafa wani kwamiti na mutum bakwai don su gudanar da bincike akan Sarkin Kano bisa wasu laifuka dai-dai har guda 8.

Cin hancin miliyan 100 da Dangote ya baiwa ‘Yan majalisar Kano don dakatar da binciken Sarkin Kano ya jawo yamutsi

Cin hancin miliyan 100 da Dangote ya baiwa ‘Yan majalisar Kano don dakatar da binciken Sarkin Kano ya jawo yamutsi

Sai dai kuma a ranar 22 ga watan Mayun, sai majalisar ta bayyana janyewa ko kuma dakatar da wannan bincike bisa roko da gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi a wata takarda da ya rubatawa majalisar, inda a cikinta ya bayyana cewa ya samu kira daga mutane daban-daban na ya dakatar da binciken da ke ci gaba da faruwa akan Sarkin kano

Cikin mutanen da gwamnan na Kano ya ambata a matsayin wadanda suke so lalle a dakatar da wannan bincike sun hada da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Aliko Dangote, Janar Ibrahim Babangida, Janar Abdussalami Abubakar, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar da dai sauran manyan kasar nan

Wani daga cikin ‘yan majalisar ta jihar Kano daya bukaci da kar a bayyana sunansa da rabon Naira miliyan 100 da Dangote ya basu bai masa dadi ba ya shaidawa jaridar Daily Nigerians cewa lalle babu ko shakka Aliko Dangote ya basu naira miliyan 100 don su dakatar da binciken, amma sai kakakin majalisar, Kabiru Rurum ya yi sama da fadi da kudin shi kadai.

Ya ce: “Jim kadan bayan mun kafa kwamitin da zai binciki Sarkin Kano sai Dangote ya bamu Naira miliyan 100 don mu dakata ta hannun kakakin majalisa.

“Amma sai kakakin majalisa ya yi shiru ya ki fadawa kowa.

"Don mun dauka ma bai karbi kudin ba har sai da asirinsa ya tonu a ‘yan kwanakin nan.

”Haka kuma dan majalisar ya bayyana cewa kakakin majalisar jihar Kano ya karbi kudade daga wajen wasu wadanda suke son a sauke Sarkin Zuwa yanzu dai ‘yan majalisar sun kafa wani kwamitin bincike akan kakakin majalisar Daily Nigerian ta tuntubi mai maganada yawun rukunin kamfanin Dangote amma sai ya ce yana halartar wani taro ne a yanzu, saboda haka babu abinda zai iya cewa.

"Sai dai kuma hukumar yaki da zamba da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta bayyana cewa ta ci gaba da gudanar da binciken ta a boye akan Sarkin Kano tun ranar da majalisa ta bayyana dakatar da nata binciken.

“Mun yi nisa wajen gudanar da wancan bincike kan Sarkin Kano kuma da zarar mun hatta maza mu mika sakamakon binciken ga gwamnan Kano”, inji wani ma’aikacin hukumar da ya bukaci da a sakaya sunansa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel