Talaka Ne Babbar Matsalar Najeriya - Inji Ministan matasa da wasanni Dalung

Talaka Ne Babbar Matsalar Najeriya - Inji Ministan matasa da wasanni Dalung

- Barista Solomon Dalung ya ce ko shakka babu talakawa sune matsalar Najeriya

- Yace duk sanda kaji wata matsala ko tashin hankali ya kunno kai to zaka samu talaka ne ya kirkiro ta

Ministan matasa da wasanni, Barista Solomon Dalung ya ce ko shakka babu talakawa sune matsalar Najeriya.

Yace duk sanda kaji wata matsala ko tashin hankali ya kunno kai to zaka samu talaka ne ya kirkiro ta saboda talaka shine bai yadda da dan uwansa ba, kuma bai yadda da addinin wani ba sannan ga bakin ciki da hassada ga junansu.

KU KARANTA KUMA: Ku haqura kuso Najeriya, ake shawartar kabilar ibo

Dalung ya bayyana haka ne a wajen taron cin abincin dare na shekara-shekara da hukumar UFUK Dialogue Foundation ta shirya a Abuja.

Sai dai babban limamin cocin katolika na Abuja, Archbishop, John Cardinal Onaiyekan, wanda shima yayi jawabi a wajen taron ya nuna jayayya da ra'ayin ministan.

A cewar Onaiyekan fitattun mashahurai da matsakaitan masu kudi sune matsalar Nigeria, yana mai cewa sune ke haddasa yawancin fitintunu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel