Ni ne zan lashe zaben shugaban kasa a zabukan 2019 - Inji Gwamna Fayose

Ni ne zan lashe zaben shugaban kasa a zabukan 2019 - Inji Gwamna Fayose

- Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya jaddada cewa shine zai lashe zaben shugaban kasa a zabukan 2019

- Fayose ya ce zai kara da shugaban kasar Muhammadu Buhari kuma ya ce shugaban zai sha kashi

- Gwamnan ya ci gaba da cewa tsofaffin gwamnonin jihar da suke son tsayawa takara wahala dai suke baiwa kan su

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose yace ko shakka babu shine zai lashe zaben shugabancin kasar nan a zabukan shekarar 2019 dake tafe.

KU KARANTA: Hukumar zabe ta kara yiwa wasu sabbin jam'iyyu 5 rajista a Najeriya

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Fayose ya bayyana haka a wani zama na musamma da yayi da mukarraban gwamnatin shi a fadar gwamnatin jihar a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni.

Ni ne zan lashe zaben shugaban kasa a zabukan 2019 - Inji Gwamna Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya ce shugaba Buhari zai sha kashi a zabukan 2019

Fayose ya ce: “ Tsofaffin gwamnonin jihar Ekiti Segue Oni, Kayode Fayemi da suke son kuma tsayawa takara a zabukan 2018 ai wahala suke baiwa kan su, ni kadai ne zan taba cin zango biyu a jihar Ekiti nima irin ayyukan dana yi ne suka bani wannan damar.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yace zai yi takara da shugaba Buhari a zabukan 2019, ko wa zai sha kayi a tsakanin su?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel