Gwamnatin Jihar Kaduna ta hana hawa babur

Gwamnatin Jihar Kaduna ta hana hawa babur

- Gwamnatin jihar Kaduna ta hana hawa babur a wasu sashi na jihar

- Hakan na da alaka da yawan sace mutane da akeyi don kudin fansa

Mai bai wa Gwamnan Jihar Kaduna shawara kan harkokin tsaro, Kanal Yusuf Yakubu Soja, ya ce majalisar tsaro ta jihar ta haramta hawa babur a wasu garuruwa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna domin a samu sukunin yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa, kamar yadda ya ce.

Babban jami'in da ke kula da ayyukan yaki da miyagun ayyuka wato (Operation Yaki), ya ce sun dauki matakin ne bayan tattaunawa a majalisar tsaro ta jihar wadda ta samu halarcin sarakuna da kuma hakiman yankin da abin ya shafa.

Ya ce dokar za ta fara aiki ne daga garin Kakau zuwa Jere wadanda suke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya ce lallai jami’an gwamnati su gana da Osinbajo

Ilyasu Umar wani wanda yake sana'ar acaba ne a garin Jere, ya ce: "A gaskiya ba mu ji dadin daukar wannan matakin ba. Da wannan sana'ar mu ke ci, mu ke sha. Idan babu wannan sana'ar za mu koma gida mu zauna ke nan."

Ya ci gaba da cewa "yan acaba ba su da hannu a satar mutane don haka bai kamata a hana mu yin acaba ba."

Hakazalika, Kanal Yusuf ya ce Babban Sufeton 'Yan Sandan kasar ya aike da jami'an 'yan sanda 600 wadanda za su rika yin sintiri a kan babbar hanyar don farauto masu garkuwa da mutane.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin arewacin kasar da suke fama da matsalar satar mutane.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel